Mas'alar Fadak



 

 Yaya kuwa annabi (s.a.w) zai ba wa Fadima (a.s) Fadak ba tare da ya ba wa sauran 'ya'yansa Zainab da Ummu Kulsum wani abu ba? Sai kwa ga shi lokacin da Bashir dan Sa'ad ya zo masa ya ce: Ya ma'aikin Allah ni ina son ba wa dana wannan lambuna kuma ina son ka shaida kan hakan. Sai Annabi (s.a.w) ya tambaye shi cewa: Shin duka 'ya'yanka ka ba su wannan? Sai ya ce: A'a. Sai annabi (s.a.w) ya ce: Tafi ni ba zan yi sheda kan zalunci ba. Sannan ga shi Annabi (s.a.w) zai ce da mutane ku ji tsoron Allah ku yi adalci tsakanin 'ya'yanku !.

 

1- Na farko: Zainb da Ummu Kulsum da Rukayya ba 'ya'yansa ba ne, wannan ita ce farkon magana domin su 'ya'yan Hala 'yar'uwar ummul Muminin Hadiza (a.s) ne da take rike su.

 

2- Ba wa sayyida Zahra (a.s) wannan Fadak ya kasance bisa umarnin Allah ne kamar yadda ya zo a littafin Yanabi'ul Fikihiyya: Sayyari ya karbo daga Ali dan Asbat cewa: Imam Musa Kazim ya zo wurin halifan abbasawa Mahadi yana neman ya dawo musu da abubuwan da aka zalunce su kansa, sai ya ce masa: Me ya sa mu ba za a dawo mana da abubuwan da aka zalunce mu kansu ba ya sarkin musulmi? Sai ya ce masa: Me ke nan ya Abul Hasan (Imam Kazim)? Sai Imam Kazim ya ce: Yayin da Allah ya yi budi ga annabinsa (s.a.w) da Fadak da kuma abin da aka samu ba tare da an kai hari kansa da doki ko wani abin hawa ba. Sai Allah ya saukar da fadinsa: Ka ba wa ma'abocin kusanci hakkinsa, annabi (s.a.w) bai san waye ba, sai ya koma wa jibril (a.s) yana tambayarsa, sai ya tambayi Allah ubangijin talikai, sai Allah ya yi masa wahayi da cewa; Ya ba wa Fatima (a.s) Fadak.

 

Sai manzon Allah (s.a.w) ya kira Fadima (a.s) ya gaya mata Allah ya umarce ni da in ba ki Fadak. Sai ta ce: Hakika na karba daga Allah kuma daga gare ka ya ma'aikin Allah. Haka nan ma ya zo a Wasa'ilus Shi'a 9: 525. Da Kanduzi: 71. Da mai littafin Mustarshid Muhammad bn Jarir Tabari: 502. Maktal Khwarizimi alHanafi a Yanabi'ul Mawadda: 44.

 

Allah (s.w.t) ya fassara ma'abota kusanci da alayen manzon Allah (s.a.w) a gurare 12, tun daga ayar nan ta gargadi ga danginsa, kuma wannan mas'alar ta zo a jerin abu na biyar a cikin littafin "Aamaali" na sheikh Mufid daga littafin Mu'ujamul Buldan. Daga littattafan 'yan Sunna akwai Majma'ul Fawa'id, da Ruhul Ma'ani na Alusi.