Neman Tabarruki



Neman Tabarruki Da Manzo Da Abin Da Ya Bari

 

Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani

Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani

Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id

 

Kadaita Allah a cikin halitta yana daya daga cikin matakan tauhidi, abin da kuwa yake nufi shi ne a wannan duniya babu wani mai halitta in ba Allah ba wanda yake shi kadai yake. Sannan dukkan abin da yake a cikin duniya na halitta a wannan duniyar ne ko kuwa a wata duniyar da ba mu gani ne Allah ne ya halicce shi, Sannan duk wani abu na halitta ba shi da samuwa ko wata kammala daga kashin kansa, idan har yana da wata kammala a zahiri to ya same ta ne daga Allah madaukaki. Dangane da wannan asali kuwa Mumini da mushiriki duk daya suke, domin kuwa a tambayoyin da Kur’ani yake kaddarawa, cewa, da za a tambayi dukkan wadannan gungu guda biyu, wato masu kadaita Allah da mushrukai a kan cewa wane ne wanda yake yin halitta, a nan amsar duka guda biyu daya take shi ne Allah ne. Ga abin da kur’anin yake cewa dangane da haka: “Da zaka tambaye su wane ne ya halicci sammai da kassai sannan ya hore rana da wata, da zasu amsa da cewa lallai Allah ne”[1].

Gurin da aka samu sabani tsakanin masu imani da mushrikai a zamanin manzanci shi ne wajen kadaita Allah a wajen tafiyar da duniya da al’amurran dan Adam, yayin da masu imani suka tafi a kan cewa Allah ne kawai yake tafiyar da duniya da abin da yake a cikinta, amma mushrikai suka tafi a kan cewa: allolin karyarsu na gumaka suma suna da hannu wajen tafiyar da duniya.

Tare da yin imani dacewa mai tafiyar da duniya da duk abin da yake a cikinta shi ne kadai Allah madaukaki, amma a lokaci guda dole ne musan cewa ba yana kore kuma tasirin wasu abubuwa ba ne a cikin wadansu abubuwan halitta. Domin kuwa bisa ga dalilai daga Kur’ani da na ilimin kimiyya da na hankali mun ga cewa duniya an halicce ta bisa wani tsari na musamman ta yadda wasu daga cikin halittu suke da tasiri a cikin wadansu, kuma wadansu abubuwa su ne dalilin samuwar wasu, don haka wasu abubuwa wadanda zasu faru sakamakon faruwar wasu abubuwa ne kafinsu. Amma dukkan wannan abin da yake a cikin duniya da tasirin da yake a tsakanin halittu yana faruwa tare da kudra da yardar Allah madaukaki. Misali hasken rana da wata, kunar wuta, da rayuwar tsirrai ta hanayar ruwa, da komai da komai, yana faruwa ne karkashin ikon Ubangiji, idan da daidai da runtsewar ido Allah zai cire ikonsa babu wani abu da zai yi saura a duniya.

Domin Karin bayani muna tunatarwa a kan cewa, a cikin wannan duniya abu guda ne kawai wanda yake shi ne sanadi na hakika, wannan kuwa shi ne Allah madaukaki, amma duk da haka a cikin wannan duniya akwai wadansu halittu wadanda suke da tasiri a cikin wasu, kuma wasu su ne sanadin faruwar wasu, amma dukkkan wannan da karfin ikon Ubangiji ne, wanda yake shi kadai ne mahaliccin duniya kuma mai tafiyar da ita. Misali girman itaciya da rayuwar mutum duk suna bisa wasu sharudda ne na duniyar dabi’a, wanda idan babu wadannan abubuwa, wadanda suka hada da ruwa, iska da haske, rayuwar dan Adam zata shiga cikin hadari. A daidai wannan lokacin wanda babu wani mai yin wani abu sai Allah, su kuwa wadannan abubuwan baki daya suna matsayin masu tafiyar da umarnin Allah ne a cikin wannan duniyar ta halitta.



1 2 3 4 next