Khalid dan Walid



A cikin abin da Khalid dan walid ya saba wa nassin shari'a na fifita ra'ayinsa da son ransa:

Abin da ya yi kawai a ranar fathu makka ya isa laifi
Abin da ya yi kawai a ranar fathu makka ya isa laifi; manzon Allah (s.a.w) ya hana shi kisa ko yaki a wannan ranar kamar yadda ma'abota sira da akhbar suka kawo, kuma masu hadisi suka tabbatar a cikin sanadodinsu ingantattu. Ya ce masa shi da zubair a ranar nan: kada ku yaka sai wanda ya yake ku. Sai dai Khalid duk da haka sai da ya yi yaki, ya kashe kusan mutane ishiri da wani abu na kuraishawa, hudu daga huzail, sai manzon Allah (s.a.w) ya shiga makka, sai ya ga wata mata da aka kashe, sai ya tambayi hanzala marubuci: wa ya kashe ta? ya ce: Khalid dan walid. Sai ya umarce shi da ya riski Khalid, ya hana shi kashe mace ko yaro, ko wani mai haya, da sauran abin da zaka samu na wannan kissar a littfin nan na (Abkariyyatu Umar) na Ukkad, shafi: 266.

Ranar yakin Juzaima
Sai Khalid ya yi wa manzon Allah (s.a.w) mufaja'a da riko mai tsanani na jahiliyya a cikin banu juzaima wannan kuwa ana gama yakin bude maka ke nan. Domin manzon Allah (s.a.w) ya aika shi zuwa gare su ne ya kira su zuwa musulunci , bai kuma aika shi don yin yaki ba. Banu juzaima sun kasance sun kashe amminsa alfakihu dan mugira a lokacin jahiliyya. Yayin da ya zo musu da shi da wadanda suke tare da shi sai ya ce musu: ku ajiye makaminku domin mutanen sun musulunta. Sai suka ajiye makamansu, sai ya yi umarni da a daure su, sai kuma ya sanya takobi ya kashe su kisa mai tsanani . Yayin da labari ya zo wurin annabi (s.a.w) sai ya daga hannunsa sama ya ce: ya Allah ni ina barranta gun ka daga abin da khalid bin walid ya yi. Har sau biyu. (Kamar yadda ya zo a littafin magazi a sahihul buhari)  .
Sannan sai manzon Allah (s.a.w) ya aika Ali (a.s) -kamar yadda ibn jarir da ibn asir ya zo a tarihinsu- tare da dukiya mai yawan gaske, ya umarce shi da ya duba lamarinsu, sai ya je ya ba su fansar diyya jini da dukiyoyi, har sai da ya biya kwatarniyar shan ruwan kare da aka fasa, kuma wata dukiya ta rage wurinsa. Sai ya ce musu: shin akwai wata dukiya da ta rage ba a bayar ba? Sai suka ce: a'aha. Sai ya ba su ragowar dukiyar kyauta don yi musu falala ya ce musu: zan ba ku wannan ragowar dukiyar saboda koyi da manzon Allah (s.a.w). sai ya yi hakan. yayin da ya dawo sai ya ba wa manzon Allah (s.a.w) labarin abin da ya yi. Sai annabi (s.a.w) ya ce: ka dace, ka kyauta. Wannan shi ne abin da masu tarihi suka kawo game da Khalid dan walid, har dai ibn abdul barr bayan nan yana cewa bayan ya kawo wannan labarin nasa a littafinsa na al'isti'ab da wannan lafazin, sai ya ce: wannan labari ne da ya ingata game da Khalid.
Kuma daga malamai marubuta da suka kawo labarin wannan kissa daga masu kiyaye tarihi akwai abbas mahmudu akkad a littafinsa na Abkariyyatu Umar ya ce: manzon Allah (s.a.w)  ya aika Khalid zuwa ga banu juzaima da ya kira su zuwa ga musulunci ba tare da ya yi yaki da su ba, ya umarce shi da kada ya kashe wani mutum idna y aga masallaci ko ya ji kiran salla. Sai banu juzaima suka ajiye makaminsu bayan wani jidali da ya faru tsakaninsu suka sallama, sai Khalid ya yi umarni da a daure su, sai ya sanya musu takobi ya kashae mutane masu yawa daga cikinsu. Daga cikin wanda suak gudu akwai wani saurayi da ake kira sumaida' da ya gudu har sai da ya shiga wurin manzon Allah (s.a.w) sai ya ba shi labari ya kai kukan abin da khalid ya yi, sai manzon Allah (s.a.w) ya tambaye shi ko wani daga mutane ya yi masa inkarin abin da ya yi. Sai ya ce: haka ne, da wnai mutum yalo matsakaici, da wani mutum ja dogo…, to umar yana wurin sai ya ce: ni na gane su wallahi ya kai manzon Allah, amma na farko shi dana ne, amma na biyun kuwa salim ne maula abi huzaifa. Bayan nan sai ta bayyana cewa Khalid ya umarce kowane mutum ya kashe wanda ya kama ribatacce, amma abdullahi dan umar da salim maula abu huzaifa sun saki nasu ba su kashe su ba…, sai manzon Allah (s.a.w) ya daga hannunsa sama ya ce: ya ubangiji ni ina barranta gun ka daga abin da khalid ya yi. Sannan sai ya kira Ali dan abi dalib ya umarce shi da ya nufi mutanen a tare da shi akwai rakuma da dukiya mai yawa, sai ya ba su fansar jini da dukiyoyin da suke gun sa.
Na ce: manzon Allah (s.a.w) bai kashe wani daga cikin wadanda suak kashe su ba, domin su makasan suna daga musulmi ne, wadanda kuma aka kashe su kuma ba su ce mun musulunta ba, sai dai sun ce mun karkace ne, ita kuwa  kalma ce da ta nuna musulunci karara, kuma ba a kashe musulmi don ya kashe kafiri.
Khalidi ya yi babn laifi ranar bidah ga malik dan nuwaira da mutanensa daga abin da masu yawa daga marubuta tarihi suka kawo shi daga ciki mun kawo wani abu daga fasalin farko na wannan littafin a shafi na 61, sai ka koma dubawa da lura, don sanin su waye suke da alhakin wadannan bala'o'in da rashin imanin da rashin tausayin, kuma yya dukiyar musulmi da jininsu da mutuncinsu ya tafi haka nan kawai, kuma don me ya sanya aka ki amfani da dokokin Allah aka keta huruminsa. Da mene ne Khalid ya kashe tawayen masu tashi da tawaye daga cikinsu akwai umar dan khaddabi. Kuma da mene ne Khalid bn walid ya fadi a idanuwan umar dan khaddabi da abin da ya sanya shi gaggautawa da  cire shi,   sai ya aika dan sako zuwa sham game da labarin wafatin abubakar tare da wasikar kawar da Khalid daga matsayinsa da mukaminsa. Kamar yadda ibn asir da waninsa suka ruwaito.
Umar ya kasance sananne ne da tsanantawa kan Khalid tun ranar bidah har sai da ya mutu, bai sanya shi kan wani aiki ba sai sau daya da ya sanya shi kan jagorancin garin kansirin wacce wani yanki ne karami, sannan sai ya maye gurbinsa da ash'as dan kais, sai ya ba shi dubu goma, sai umar ya ji hakan, kuma wani abu daga aikin Khalid ba ya buya gare shi, sai umar ya kira dan sako ya rubuta masa wasika tare da shi zuwa ga abi ubaida –wakilinsa na hims-: a ciki umar ya rubuta cewa: Ka tsayar da Khalid kan kafa daya, dayar kuma a daure ta da rawaninsa, sannan ka cire masa hularsa a gaban shedu, daga masu aikin daula da manyan garin, har sai ya sanar da ku daga ina ne ya ba wa ash'as kudi, shin daga dukiyarsa ne? idan haka ne Allah ba ya son masu barna, ko kuwa daga dukiyar daula ce? Wannan sunansa ha'inci, Allah kuwa ba ya son masu ha'inci, kuma ko meye dai ka cire shi, ka hada aikinsa da naka.
Sai abu ubaida ya aika wa Khalid cewa ya zo yana neman sa, sai ya zo, sai ya tara masa mutane, ya zaunar da su yana kan mimbari  a masallacin garin, sai dan sako ya tashi ya tambayi Khalid: daga ina ne asha'as ya samu wannan? Sai bai amsa ba, abu ubaida kuwa yana zaune yana shiru ba ya cewa komai. Sai bilal habashiya tashi ya ce: sarkin muminai ya yi umarni da abu kaza da abu kaza a kanka, sai ya cire masa rawani, ya sauke hularsa, sannan sai ya tsayar da shi ya daure masa kafa daya da shi, sannan sai ya ce masa: daga ina ne ka samu abin da ka ba wa ash'as? daga dukiyarka ne? ko daga dukiyar mutane? Sai ya ce: daga dukiyata ne. sai ya kwance shi ya mayar masa da hularsa, sannan sai ya sanya masa rawani da hannunsa, sai ya ce: muna ji muna bi ga jagororinmu ne, kuma yin hidima ga barorinmu ne. sai Khalid ya tsaya yana mai dimaucewa bai sani ba, shin an sauke shi ne ko kuma ba a sauke shi ba, domin abu ubaida bai sanar da shi sauke shi ko rashin sauke shi ba. Yayin da ya jinkirta zuwansa gun umar sai abin da ya yi tsammani ya wakana, sai ya rubuta wa Khalid cewa an sauke ka, ka bayar da wuri. Sannan umar bai sake ba shi wani aiki ba har ya rasu .      
Kuma ukkad ya faru wannan lamarin a littafinsa na abkariyyatu umar shafin na 269 game da khalida yana cewa: Khalid ya ba wa ash'ass dan kais mawaki dirhami dubu goma sai aka gaya wa umar labari kamar dai yadda aka saba ba wa umar labaran ma'aikatansa na jagorori da wakilai ta hannun 'yan leken asirinsa da masu yi masa leke, sai ay rubuta wa abu ubadai ya yi wa Khalid bincike kan lamarin kyautar da ya bayar, idan ya ce daga wata kyauta ce da ya samu to ya yi furuci da ha'inci, idan kuwa ya yi furuci da cewa daga dukiyarsa ce, to ya yi israfi a dukiayrsa.
Da farko dai Khalid ya ki amsawa sai abu ubaida ya kama shi da rawaninsa ya daure shi kamar yadda umar ya yi umarni, sai kuma ya cire masa hula a wannan matsayin na bincike, har dai ya ce: daga dukiyarsa ne. ya ce: sai aka yi kimar kayansa aka kara abin da ya dadu a kai cikin baitul mali.
Na ce: Khalid ya kasance yana da wani lamarin kuma tare da umar a lokacin abubakar har umar ya tsananta wa Khalid a kan ta, wannan kuwa ibn sa'ad ya kawo shi a cikin littafinsa na dabakat, haka ma ibn abi shaiba a littafinsa na sunan, da abdurrazak a jami'nsa, haka nan almuntaki alhindi ya kawo shi a shafi na 29 a juzu'I na shida na kanzul ummal.
Haka nan wasunsu ma sun ruwaito daga urwa dan zubair ya ce: Khalid dan walid ya kona wasu mutane da wuta daga ma'abota ridda. Sai umar ya ce da abubakar: shin za ka bar wannan yana azabtar da mutane da azabar Allah? Sai abubakar ya ce: ba zai dakusa takobi ba da Allah ya wasa shi kan mushrikai.
Duk wanda ya san halin umar , ya san cewa ya kasance ba ya iya jure wa barnar wadanda suek manya ne daga jama'arsa wadand suke da wata barna da suka yi kamar Khalid dan walid da makamantansa, sai ya yi dakunsu don ya kama su a farkon abin da suka yi na keta hurumin shari'a don ya kama su da wannan, sannan ba ya yi musu afuwa kamar yadda ya yi wa Khalid.
Wannann ita ce dabi'a rayuwarsa lokacin da yake halifanci da ta faru da yawa wacce ba ta buya ga masu bin wannan lamarin.