Rikicin Jagoranci



 

Fasali na hudu

Wasu abubuwan da aka ruwaito game da a'isha  na abin da ta yi tawilinsa na nassin shari'a a fili, kuma ba ta yi aki da abin da yake daidai ba, kawai sai ta yi aiki da abin da ta gani na kanta

 
(69)
Abin da ya ta yi na fita kan yakar Imami tana mai neman jinin usman , bayan ta dora masa nauyin sakamakon abin da ya yi, ta cuna mutane su kashe shi, da kuma maganganun da ta yi kansa
Allah madaukaki yana fada a cikin abin da ya yi wa matan annabi (s.a.w) umarni da shi a cikin littafinsa a ayyoyi muhkamai daga surar ahzab cewa: "Ku tabbata a gidajenku, kuma ka da ku fita irin fitar jahiliyya ta farko, kuma ku tsayar da salla kuma ku bayar da zakka, kuma ku bi Allah da manzonsa" ahzab: 33.
Sai dai sayyida a'isha ta fita kan yakar Imami bayan an yi masa bai'a da haduwar ma'abota iko da zartarwa a kan yi masa bai'a, kuma farkon wnda ya yi masa bai'a shi ne dahla da zubair da sauran wadanda suka rigaya na farko da sauran su.
Sai ta fita don ta yake shi daga gidan da Allah ya umarce ta da ta zauna a cikinsa, kuma ta fita a kan rakumi, tana jagorantar sama da karti dubu uku da wawayen larabawa, daga cikinsu abin takaici akwai dalha da zubair, wadanda su kuma suka warware bai'a, tana hawa da rundunarta kan duwatsu da kwari, tana wuce saraki da dazuzzuka, har sai da ta isa basara wacce taek karkashin jagorancin wakilin Imam Ali usman dan hanif al'ansari, sai ta bude ta da zubar da jini mai yawan gaske, da keta hurmomin al'umma, abubuwan rashin imani masu ban al'ajabi sun faru a nan wadanda marubutan tarihi suka kawo su dalla-dalla, kuma ana kiran wannan yakin da harin da ta kai basara da yakin jamal dan karami, wannan kuwa ya faru ne a biyar ga watan rabi'us sani sheka ta talatin da shida hijira, wannan kuwa ya faru kafin Imam Ali (a.s) ya zo basara ne.
Sannan sai yayin da Imam Ali ya zo basara tare da wanda suke tare da shi, sai a'isha ta sake fitowa da wadanda suke tare da ita suna kore shi daga garin suna nisantar da shi, sai ya kame ya ki yakar ta, ya kirata zuwa ga yin sulhu da maganar da duk wnai mai hankali zai yarda da ita, sai dai ta dage a kan sai ta yi yaki, ta fara kai masa hari, sai ya kasance a lokaicn ba abin da zai iya yi sai ya kare kansa a aikace da fadin Allah madaukaki cewa: "ku yaki wacce take zalunci har sai ta koma zuwa ga lamarin Allah" hujurat: 9.
Da wannan ne Allah ya yi masa budi, sai dai bayan yaki mai tsanani da musulmi suka yi sai aka kira wannan ayakin da yakkin jamal babba, wanan kuwa ranar alhamis ne goma ga wata jimada akhir shekarata ta talatin da shida bayan hijira, wannan yakoki biyu sai ya kasance sun shahara matuka irin shahara da yakin siffain da nahrawan da badar da uhud da ahzab suka yi, masu tarihi sun kawo labarin su dalla-dalla a cikin yakokin da suka faru a shekara ta talatin da shida bayan hijira , kuma yawancin wadanda suka kawo labarin tarihin Imam Ali (a.s) ko a'isha sun kawo tarihinsu tare da tarihin sauran sahabbai da tabi'ai da suak halarta .
Game da wannan abin haushi
Duk masu tarhi da ruwayoyi sun kawo wanna lamarin da bin abil hadid ya kawo a sharhinsa na nahajul balaga cewa :  a'isha ta kasance daga cikin wadanda suka fi kowa tsanantawa usman, hari sai da ta fitar da wani littafi na manzon alah (s.a.w) ta kafa shi an dakinta tana cewa da masu shiga wurinta: wannan tufafin manzon Allah (s.a.w) ne bai tsufa ba, amma usman duk ya lalata sunnarsa. Suka ce: ita a'isha ce farkon wanda ya kira usman da na'asal. Ta kasance tana cewa: ku kashe na'asal Allah ya kashe na'asal, ku kashe na'asal lallai ya kafirta. Kuma dalha da zubair suna cikin masu tsananin cuna masa mutane, dalha ya fi su tsanantawa. Mada'ini ya ruwaito a cikin littafin jamal da sauran masu tarihi duk suka kawo cewa: yayin da aka kashe usman a'isha ta kasance a makka ne, yayin da labarin kashe shi ya zo mata ba ta taba tsamamnin cewa ba dalha ne zai zama jagora ba, sai a ce: kaicon na'asal tir da shi, madalla da damar da mai 'yan yatsu ya samu, madalla da baban shibl, madalla da dan ammi, kai ka ce ina ganin sa ya sanya 'yan yatsunsa ana yi masa bai'a. (tana mai albishi da cewa dalha ya samu damar zama halifa ke nan), dalha ya kasance ya karbe makullan baitul mali yayin da aka kashe usman, kuma ya karbe duk wani abu na usman da yake gidansa, sannan yayin da bai samu damar jagoranci ba, sai ya mika su hannun Ali.
Dabari da waninsa sun ruwaito da sanadi zuwa ga asad bn abdullahi daga wadanda suka riska na daga ma'abota ilimi cewa ; yayin da a'isah ta kai zuwa ga siraf tana mai dawowa a kan hanyarta ta makka, sai ta hadu da abdu dan ummu kilab, shi bawa ne na ibn ummu salama da ake danganta shi zuwa ga babarsa, sai ta ce masa: me ye labara. Sai ya ce: sun kashe usman sun zauna kwana takwas. Ta ce: sai kuma suka yi me? Sai ya ce: mutanen madina suna kama ta gaba daya, sai kuma suka kai ga mafi kyawun lamarin da ya dace, sai suka hadu a kan zabar Ali dan abu Dalib. Sai ta ce: Ina ma dai wannan (sama) ta fado kan wannan (kasa), idan dai sahibinka ne (wato Ali) aka zaba, to ku mayar da ni makka, ku mayar da ni, ku mayar da ni. Sai ta koma makka tana cewa: wallahi an kashe usman abin zalunta ne, wannan sai na nemi yaki da sunan jininsa. Sai dan ummu kilab ya ce mata: saboda me? Wallahi ke ce farkon wanda ya fara yi masa cune ke ce. Ke ce kike cewa a kashe na'asal ya kafirta. Sai ta ce: ai sai da suka nemi ya tuba sannan sai suka kashe shi, kuma ni na fada, su ma sun fada, amma maganata ta karshe ta fi ta farko. Sai dan ummu kilab ya ce mata:
Daga gare ki ne farko, daga gare ki ne canji
Daga gare ki iska take, daga gare ki ne ruwan sama
Ke ce kika yi umarni da kashe Imami jagora
Kuma kika ce da mu ya riga ya kafirta kuma
Sai muka ta shi muka bi ki a kisan sa kuma
Mai kashe shi a cikinmu ya yi ne da umarnin
Kuma safa ba ta fado a kan kawukanmu ba
Kuma ranarmu ba ta kisfe mana ba haka ma wata
Kuma mutane sun yi wa mai ilimi da la'akari bai'a
Yana kawar da zalunci yana tsayar da adalci
Kuma yana sanya wa yakoki tufafin yin su
Mai cika alkawari ba kamar mai yaudara ba ne
Ya ce: sai ta koma makka, ta sauka a kofar masallaci, sai ta nufi daki , mutane suka taru wurinta, sai ta ce: ya ku mutane an kashe usman abin zalunta, wallahi ni zan nemi jininsa, sai ta tayar da wata makauniyar fitina kurma bebiya domin kawai ta huce haushinta kan masoyin annabi (s.a.w) Imam Ali (a.s) wanda ya kebanta da 'yan'uwantaka da annabi (s.a.w), kuma ya kasance shi ba mai kisa ga usman ba, shi kuma ba wanda ya kwadaitar da a yi kisan ba, ba kuma mai yarda da kisan ba . Daga cikin abin da ta fada kamar yadda ya zo a cikin littafin alkamil na ibn asir ; wawaye sun taru daga garuruwa, da masu ruwa, da bayin mutanen madina, sai suka taru kan wannan mutumin suka kashe shi bisa zalunci, suka yi masa ukubar sanya  samari da ya yi kan aikin al'umma alhalin wadanda suke kafinsa sun snaya irinsu aiki. Da kuma yanke jeji da bayar da shi, amam sai ya tuba daga dukkan wannan. Ba su samu wata hujja kansa ba, ko wani uzuri, sai suka yi masa shisshigi suka zubar da jininsa mai alfarma, suka halatta gari mai alfarma, da wata mai alfarma, suka kwashe dukiya mai alfarma, wallahi dan yatsa daya na usman ya fi cikin duniya baki daya da ire-irensu, kuma na rantse da Allah da abin da ya yi musu na laifi da suka kash eshi a kai ya kasance laifi ne to da ya fita daga cikinsa kamar yadda ake tsarkake zinare daga tuttukarsa, ko tufafi daga daudarsa, yayin da suka cukukkuda shi kamar yadda ake cukukkuda tufafi da ruwa.  Sai abdullahi dan amir alkhadharami ya ce: ya kasance yana wakilin usman ne a makka: ni ne farkon wanda zai nemi wannan fansar jinin. Kuma banu umayya suka bi shi a kan hakan, sun kasance sun gudu daga madina zuwa makka bayan kashe suman ne.
Matakin ummu salama a wannan fitina
Masu tarihi sun kawo cewa kamar yadda ya zo a shafin na 77 da abin da yake bayansa na mujalladi na biyu na sharhin nahajul balaga na Hamidi ya ce: a'isha ta zo wurin ummu salama don ta yaudare ta kan fita domin neman jinin usman, sai ta ce mata: ya ke 'yar abi umayya, ke ce farkon wacce ta yi hijira daga matan annabi, kuma ke ce mafi girman uwayen muminai, kuma manzon Allah (s.a.w) yana kasa mana kwana tare da ke, kuma yawanci jibril yana zo masa ne idan yana dakinki. Sai ummu salama ta ce mata: saboda wani abu ne kika fadi wannan maganar! Sai a'isha ta ce: mutane sun nemi tuban usman , sai da ya tuba sai suka kashe shi yana mai azumi a wata mai alfarma, kuma na yi niyyar fita zuwa basara da wanda yake tare da ni na zubair da dalha, ki fita tare da mu, ta yiwu Allah ya gyara wannan lamarin a hannunmu. Sai ummu salama ta ce: ke ce jiya kike kara kina tara masa mutane don su gama da shi, kina fadin mafi munin magana a kansa, kuma ba shi da wani suna gun ki sai na'asal, kuma kin san matsayin Ali (a.s) gun manzon Allah (s.a.w), ko in tuna miki? Sai a'isha ta ce: tuna mini. Sai ummu salama ta ce: kin tuna wata rana da Ali (a.s) ya zo mu muna tare da manzon Allah (s.a.w) sai ya sauka a kadidi daurar hagu sai ya kebe da Ali yana tattaunawa da shi, sai ya tsawaita, sai kika yi nufin ki hayayyake musu (manzon Allah da Ali), sai na hana ki, kika kuma saba mini da yin hujumi kan su, sai ga shi kin dawo kina kuka. Sai na ce: me ya same ki. Kika ce mini: na je suna ganawa ne, sai na da Ali ni ba ni da wata rana tare da manzon Allah (s.a.w) sai rana daya daga cikin tara, shin ya kai dan abu dalib ba za ka kyale mini ranata ba? Sai manzon Allah (s.a.w) ya fuskanto ni fuskarsa tana cike da fushi ya ce: koma inda kike fito, Allah ba ya fushi da wani daga mutane sai ya fita daga imani. Sai kika dawo kina nadama da bakin ciki. Sai a'isha ta ce: na'am haka ne. umma salama ta sake cewa: Ina tuna miki wani abu kuma: wata rana na kasance da ni da ke tare da manzon Allah (s.a.w) sai ya ce da mu: wace ce a cikinku mai rakumi mai yawan gashi  da karnukan garin hau'aba zasu yi wa haushi, sai ta kasance wacce ake kifar da ita a kan siradi ranar lahira? Sai muka ce: muna neman tsarin Allah da manzonsa daga wannan, sai ya doki bayanki ya ce: ina hana ki zama ita ce ya ke 'yar ja. Ummu salama ta ce: ni dai na yi miki gargadi da nasiha. A'isha ta ce: na tuna wannan. Sai ummu salama ta ce: ki tuna ranar da na kasance da ni da ke tare da manzon alah (s.a.w) a wata tafiya tasa, Ali ya kasance yana gyara takalmin manzon Allah (s.a.w) da tufafinsa yana wankewa, sai takalminsa ya cire, sai Ali ya tsaya wata rana yana gyarawa ya zauan cikin wata inuwar bishiyar magarya, sai babanki da umar suka zo, sai muka tashi muka sanya hijabi, sai suka shiga suna yi masa magana, ba su gushe ba har sai da suka ce: ya ma'aikin Allah , mu ba mu san iyakacin muddar da zaka kasance cikinmu ba, da ka sanar da mu, sai a sanya mai halifancinka a kanmu, don ya kasance wanda zamu koma masa bayanka. Sai ya ce musu: ni ina ganin wurinsa, kuma da na yi hakan da kun waste kun bar ni kamar yadda banu isra'il suka waste daga harun (a.s). sai suka yi shiru suka fita. Bayan sun fita, sai muka fita zuwa manzon Allah (s.a.w) sai kika ce masa domin kin fi mu jur'a kan manzon Allah (s.a.w): ya ma'aikin Allah wa ye zaka bari halifa kan mu:? Sai ya ce: mai gyara takalmi. Sai muka sauko sai muka ga Ali ne. sai kika ce: ba na ganin kowa sai Ali. Sai manzon Allah (s.a.w) ya ce: ai shi ne. sai a'isha ta ce: na tuna wannan. Sai ummu salama ta ce mata: wane fita kuma zaki yi kansa bayan wannan ya ke a'isha. Sai ta ce: ni dai zan fita don gyara tsakanin mutane.
Ummu salama ta zo mata bayan nan kamar yadda abu Muhammad abdullahi dan muslmi dan kubaiba ya kawo a littainsa na musannaf fi garibil hadis ya ce: sai ummu salama ta hana ta fita da magana mai tsanani da ya kwo a ciki cewa: ginshikin musulunci ko da ya karkace ba a iya gayra shi da mata, kuma ba ya daidaita shi da su idan ya yi tsaga, yabon mata shi ne rufe idanuwa, da kiyaye mutunci. Me zaki ce  da annabi (s.a.w) da ya same ki a cikin wannan dajin kina mata tafiya kwararoro kwararo daga masauki zuwa wani masauki? Wallahi! Da na yi wannan lamarin naki sannan aka ce mini in shiga Firdausi da na ji kunyar in hadu da Muhammad ina mai keta hijabin da Allah ya sanya mini shi, har dai zuwa karshen maganarta gare ta wacce a'isha ba ta saurare ta ba .
A lokacin ne sai ummu salmaa ta rubuta wa Imam Ali (a.s) wasika daga makka, bayan haka: dalha da zubair da jama'arsu daga mabiya bata suna son su fita tare da a'isha a tare da su akwai abdullahi dan amir, suna masu cewa an kashe usman abin zalunta ne, Allah zai isar musu da dubararsa da karfinsa, ba don dai Allah ya hana mu fita ba, kuma kai ba ka yarda da shi ba, don in fita in taimaka maka, sai dai ni zan aiko maka da dana wanda yake shi ne kamar matsayina umar dan abi salama, zai halarci dukkan yakokinka tare da kai, ka yi masa wasiyya da alheri ya kai jagoran muminai, yayin da umar dan abi salama ya zo wurin Ali (a.s), bai gushe tare da shi ba, har sai da ya halarci dukkan yakokinsa tare da su.
Matakin Hafsa:
A'isha ta aika wa hafsa da sauran uwayen muminai kamar yadda masu tarihi suka kawo tana rokon su da su fito tare da ita zuwa basara , babu wacce ta amsa musu a cikinsu sai dai hafsa kawai, sai dai dan'uwanta abdullahi ya zo ya hana ta fita, sai ya sauke kayan tafiyarta bayan ta dora su .
Matakin  Malik al'Ashtar:
Al'ashtar ya rubuta wa a'isha wasika tana makka a lokacin cewa: bayan haka; ki sani ke matar manzon Allah (s.a.w) ce, kuma ya umarce ki da ki zauna a gidanki, idan kika yi haka shi ya fi ye maki, idan kuwa kika ki sai kin dauki tufafinki, kin sanya mayafinki, kin bayyana wa mutane gashinki,  to zan zo in yake ki har sai na mayar da ke gidanki, inda nan ne wurin da ubangijinki ya yardar miki ki zauna.
Jagorancin wannan fitinar:
Jagaorancin wannan yakin gaba daya yana hannun a'isha ne, ita ce take bayar da umarni , take tsara hari, da ayyana jagorori da kwamandoji, da cire wanda ta so , da kuma rubuta wasiku da yada su cikin musulmi tana neman su tashi su yaki Imam Ali (a.s) , tana neman su taimaka mata, sai wanda ya amsa mata ya amsa, wasu jama'a masu baskira da hankali suka yi raddin abin da take nema, sai dai banu umayya sun bayar da kokari matuka don wannan fitowa da yakar Imam Ali da dukkan dukiyoyinsu, suka kuma yada ta a ko'ina duk inda zasu iya, marwan ya kasance a cikin rundunarta, sai dai ya kasance yana harba kibiyarsa cikin duka runduna biyyu wani lokaci rundunarta, wani lokaci ya harba cikin rundunar Ali (a.s), yana cewa duk wacce na samu budi ne, har ma ana cewa shi ne wanda ya harbe dalha.
Fitowar a'isha daga makak zuwa basara:
Yayin da a'isha ta futo daga makka zuwa basara sai ta tara banu umayya da masoyansu suka yi musayar ra'ayi, sai wasu suka ce mu je mu samu Ali mu yake shi, sai a'isha da wasu jama'a suka ce: ba zaku iya yakar mutanen madina ba. Sai wasu suka ce: mu tafi sham. Sai a'isha da wasunsu suka ce: mu'awiya ya isar muku shama, sai dai mu tafi basara mu shige ta, da kuma garin kufa, domin dalha yana da fuska gun mutanen kufa, shi kuma zubairu yana da masoya a mutnen basara, sai suka yi ittaifaki kan hakan.
Yayin nan ne sai abdullahi dan amir ya bayar da dukiya mai yawan gaske da rakuma masu yawa, kuma ya'ala dan umayya ya taimaka musu da dubu dari hudu, kuma ya ba su mahaya saba'in , kuma ya dora a'isha kan wani rakumi da ake kira askar, ya kasance babba ne matuka mai tsanani. Yayin da ta ji sunansa sai ta yi istirja'I ta ce: ku mayar da shi ba na bukatar sa, ta fadi cewa manzon Allah (s.a.w) ya gaya mata wannan sunan, kuma yana ta hawansa. Sai mutane suak nemo mata waninsa ba su samu mai kama da shi ba, sai suka canja masa kayan ado suka kawo mata shi, suka ce: mun samo wani wanda ya fi shi girma da karfi. Sai ta samu kwanciyar hankali ranta ya kwanta da shi , ba ta fita daga makka ba har sai da ta samu duk wani irin taimako da zata iya samu daga banu umayya na taimako sannan sai ta wuce ta kama hanyarta.
Ruwan Hau'aba:
Manyan malamai daga masu tarihi sun ruwaito daga usam dan kuddama daga ikrama daga ibn abbas daga manzon Allah (s.a.w) cewa, manzon Allah (s.a.w) ya gaya wa matansa wata rana suan tare baki daya wuri daya cewa: wace ce mai rakumi mai yawan gashi, da karnukan Hau'aba zasu yi musu haushi, kuma a kashe jama'a masu yawan gaske a hannunta na dama da na hagunta, dukkan su su shiga wuta, ita kuwa ta tsira da kyar? .
Masu tarhi sun ruwaito cewa: yayin da a'isha  ta kai ruwan garin Hau'aba , wani ruwa ne na banu amir bn sa'asa'a, sai karnunka suka taso mata da haushi har sai da rakumanta masu tsanani suak hargitsa. Sai wani daga jama'arta ya ce: ba ku ga yawan  karnukan garin hau'aba da yawan haushinsu ba. Sai uwar muminai ta tsaya ta dakata da rakuminta ta ce: shin su ne karnukan hau'aba? Ku mayar da ni, ku mayar da ni! Na ji manzon Allah (s.a.w) yana cewa: … sau ta fadi sauran hadisin.
Sai wani mai magana ya ce mata: Allah ya yi miki rahama ai mun wuce ruwan garin Hau'aba. Sai ta ce: waye zai yi maka sheda? Sai suka kawo mutanen hamsin daga larabawan yanki suka ba su kudi, sai suka zo suka rantse mata a kan cewa nan ba ruwan hau'aba ba ne . sai ta wuce har sai da ta zon zuwa Hafru Abi Musa kusa da basara.
Matakin abul aswad addu'Ali ga a'isha da dalah da zubair
Yayin da a'isha ta kai zuwa gari hafru abi musa da rundunarta sai usman dan hanif ya aika abul aswad addu'ali zuwa ga mutanen don ya san labarinsu, sai ya shiga wurin a'isha ya tambaye ta inda za ta. sai ta ce: ina neman jinin usman ne. sai ya ce: ai a basara babu wani daga makasa usman. Sai ta ce: ka yi gaskiya, sai dai su suna tare da Ali dan abu daliba madina, kuma na zo ne ina neman taimakon mutanen basara don yakar sa, a yanzu zamu yi fushi da usman saboda ku, kuma ba zamu yi fushi da takobinku saboda usman ba?!. Sai ya ce mata: ke me zaki yi da bulala da takobi, ke fa tsarewar gidan manzon Allah ce da ya yi umarni da ki zauna a gidanki, ki karanta littafin ubangijinki, kuma babu yaki a kan mata, ba sa neman jini, kuma jagoran muminai Ali (a.s) shi ne ya fi cancanta da jinin usman fiye da ke, shi ne ya fi ki kusancin jini da shi fiye da ke, ki sani su 'ya'yan abdu manaf ne. sai ta ce: ni ba mai juyawa ba ce har sai na zartar da abin da na zo yi, shin ya kai abul aswad kana tsammani wani zai zo ya yake ni?! Ya ce: amma wallahi mu zamu yake ki yakin da mafi saukinsa mai tsanani ne.
Sannan sai ya tashi ya zo wurin zubair ya ce: ya kai baban abdullahi mutane sun san ka ranar da aka yi wa abubakar bai'a kana rike da takobinka kana cewa: babu wani wanda ya fi cancanta da wanan lamarin fiye da Ali dan abu dalib, ina wannan matakin da ka dauka da na yau? Sai ya gaya masa cewa: jinin usman. Sai ya ce: ai kai da sahibinka (dalha) ku ne kuka yi masa hakan bisa abin da ya zo mana labara. Ya ce: sai zubair ya ce wa abul aswad je ka wurin dalha ka ji me yake cewa. Sai ya tafi wurin dalhar sai ya same shi yana kan bakansa na shisshigi da zalunci (ga Imam Ali) yana mai dagewa a kan sai an yi yaki da fitina. Sai abul aswad ya koma ya gaya wa usman dan hanif abin da ake ciki na shirya wa yaki, ya gaya masa ya shiriya.
A'isha da ibn sauhan:
A'isha -tana basara- sai ta rubuta wa zaid dan sauhan al'abdi wasika cewa: daga a'isha uwar miminai 'yar abubakar siddik, matar manzon Allah (s.a.w), zuwa ga danta mai ikhlasi zaid dan sauhan.
Amma bayan haka, ka zauna gidanka, ka hana mutane taimakon Ali dan abu dalib, kuma ina son labarin da nake so ya zo mini daga gare ka, domin kai ne mafi amnincin ahalina guna, wassalam.
Sai ya amsa mata –kamar yadda ya zo a sharhin nahajul balaga na ibn abil hadid- da cewa: daga zaid dan sauhan zuwa ga a'isha 'yar abubakar.
Amma bayan haka, hakika Allah ya umarce ki da wani lamari, kuma ya umarce mu da wani lamarin, ya umarce ki da zama gidanki, kuma ya umarce mu da yin yaki, kuma wasikarki ta zo mini tana umarta ta da abin da yake sabanin abin da Allah ya umarce ni da shi, sai ya kasance na yi abin da Allah ya umarce ki da shi, ke kuma kin yi abin da Allah ya umarce ni da shi, lamarinki guna ba abin bi ba ne, kuma wasikarki ba ta da amsa.
Jariya dan kuddama assa'adi da a'isha:
Dabari ya ruwaito da sanadi zuwa ga kasim dan Muhammad dan abubakar cewa ya ce : jariya dan kuddama assa'adi ya zo wurin a'isha sai ya ce: ya babar muminai wallahi kashe usman dan affana ya fi sauki daga fitar ki daga gidanki a kan wannan rakumin la'ananne da sanya kan ki wurin makami, ki sani kina da sutura da hurumi gun Allah, sai kika keta wannan suturar, kika halatta wannan huruminki, domin duk wanda ya ga yakinki, to yana ganin kisanki, idan kin fito ne da kanki, to ki koma gidanki, ama idan kin fito ne bisa tilasi to ki nemi taimakon mutane.
Wani saurayi ma daga banu sa'ad yana mai sukan dalha da zubair yana ce musu:
Kun boye matanku kun gabatar da babarku
Wannan lamarin wallahi karancin adalci ne
Ku yi umarnin jan zaninta tun daga gidanta
Sai ta rika keta sarari a jejin dazuka
Abin yaka da 'ya'yanta suke yaki don ita
Da kwari da kibiya, da mashi da takubba
Sai aka keta suturarta sanadin dalha da zubair
Wannan shi ne labari game da su, kai! Ya isa
Wani saurayi daga kabilar juhaina da Muhammad dan dalha:
Wani bajuhaine ya zo wurin Muhammad dan dalha sai ya ce: ba ni labari game da makasa usman. Sai ya ce: jinin usman gida uku ne: sulusi kan mai hawan rakumi wato a'isha. Sulusi kan mai jan rakumi yana nufin babansa dalha. Sulusi kuma kan Ali dan abu dalib. Sai wannan saurayi bajuhaine ya yi dariya ya riski wurin Imam Ali (a.s) yana cewa:
Na tambayi dan dalha kan halakakke
A cikin madina da ba a yi wa kabari ba
Sai ya ce: jama'a uku ce wadanda su ne
Suka kashe dan affana sai ka lura fa
Sulusi yana kan wacce take dakin aure
Sulusi kuwa yana kan mai jan rakumi
Sulusi kuwa yana kan dan abu Dalib
Kuma mu ne dai kauyawan karkar
Sai na ce masa ka yi gaskiya kan na farko
Amma ka yi kuskure a kan na uku mai haske
Ahnaf dan kais da a'isha:
Baihaki ya ruwaito a cikin littafin "almahasin wal masa'wi" (juzu'I na 1, shafi: 35) daga hasanul basari cewa:  ahnaf dan kais ya ce da a'isha ranar yakin jamal: ya ke uwar muminai, shin kina da wani abu da manzon Allah (s.a.w) ya ba ki umarnin sa a kan wannan tafiyar? Sai ya ce: wallahi babu. Sai ya ce: kin yi gaskiya, Allah ya yardar miki da mutanen madina ke kuma kin ki yarda sai dai mutanen basara, kuma ya umarce ki da ki zauna gidan annabinsa (s.a.w) sai kika ki sai dai gidajen banu dhubba. Shin ba kya ba ni labari ba ya uwar muminai kin zo yaki ne ko kin zo sulhu? Sai ta amsa tana mai jin zafin tambayar? Na zo sulhu ne. sai ya ce mata: wallahi kin zo wurinsu babu ko duka da takalmi ko jifa da duwatsu, ba su gyaru a hannayenki ba, yaya kuwa zasu gyaru alhalin takubba suna kan wuyansu?. Sai ta ji haushi tana mai cewa: zuwa ga Allah ne nake kai kukan rashin biyayyar 'ya'yana.
Abdullahi bn Hakim attamimi da dalha:
Abdullahi dan hakim ya zo yana mai hada dalha da Allah yana mai cewa : ya kai baban Muhammad amma wannan kuwa ba wasikunka ba ne zuwa gare mu? Sai dalha ya ce: haka ne. sai ya ce: ka kira mu jiya kana mai neman mu cire usman da yakar sa, har sai da ka kashe shi, kuma sai ka zo mana kana neman fansar jininsa! Meke nan wannan ra'ayin naka, ba komai kake nema ba sai wannan duniyar, to ka yi sannu sannu. Me ya sa ka karbi abin da Ali ya nema daga gare ka na yin bai'a, sai ka yi masa bai'a kana mai biyayya gare shi mai yarda, sannan sai ka warware bai'arka, kuma ka zo don ka shigar da mu cikin fitinarka? Sai ya ce: Ali ya kira ni zuwa ga yi masa bai'a ne bayan mutane sun yi masa bai'a . Sai na san cewa idan ban karbi abin da ya nema daga gare ni ba, to babu wani abu da zan samu, sannan sai ya cuna mini wadanda suke tare da shi.
Hakim daga banu jashm yana yi wa mutanen basara nasiha:
Yain da a'isha da wadanda suke tare da ita suka kai wurin da ake kira Marbad –kusa da basara- sai aljashami ya tashi yana yi wa mutanen basara huduba da suka taru a ann yana cewa : ni ne wane dan wani aljashami kuma wadannan mutanen zun zo muku, idan sun zo muku suna masu jin tsoro ne, to sun zo muke ne daga wurin da tsuntsu ma da dabbobin jeji da zakoki suke cikin aminci, amma idan kuma sun zo muku ne suna neman jinin usman ne, to waninmu ne shi ne ma'abocin jininsa ba mu ba, don haka ya ku mutane ku bi ni, ku mayar da su ta inda suka fito, ku sani idan ba ku yi haka ba, to ba zaku kubuta daga yaki mai tsanani ba, da kurmar fitina, sai wasi daga mutanen basara masu goyon bayan ma'abota fitinar jamal (rakumin a'isha) suka jefi shi da tsakuwa.
Bayanin a'isha ga mutanen basara:
Sannan sai a'isha ta gabato kan rakuminta askar, sai ta yi shela da sauti mai karfi  ya ku mutane ku yi karancin magana ku yi shiru, sai mutane suak yi shiru. Sai ta ce: ya ku mutane hakika sarkin muminai usman ya canja ya jirkita, amma sai ya kasance bai gushe ba yana wanke wannan kurakuran da tuba har sai da aka kashe shi abin zalunta yana mai tuba, kuma kawai sun yi masa haka ne saboda bulala da yake yi da samari da yake sanya  wa kan lamuran al'umma, da kangewarsa ga wurin Gamama, sai suka kashe shi a harami, cikin hurumin wata, da hurumin gari da yanka kamar yadda ake yanka rakumi. Ku sani kuraishu ta harbi kanta da kibiyarta, kuma ta sanya zubar jini a bakinta da hannayenta, kuma ba ta samu komai ba da kashe shi da ta  yi, ba ta kuma shiga wani tafarki ba tana mai nufin gaskiya, amma wallahi sai sun ga bala'o'I masu muni da zasu farkar da na tsaye, su sanya na zaune mikewa tsaye, kuma da sannu Allah zai sallada musu wasu mutane da ba sa jin tausayin su, su dadana masu dandanun azaba mai radadi. Ya ku mtuane ku sani laifin usman bai kai ga babin da zai zubar da jininsa ba, sun yamutsa shi kamar yadda ake yamutsa tufafi mai arha, sannan sai suka yi masa ketare iyaka suka kashe shi bayan ya tuba, da fitarsa daga zunubinsa, sai kuma suka yi wa dan abi dalib bai'a ba tare da shawarar jama'a ba don cin fuska da kwace.
A yanzu kuna ganin zan yi fushi da bulalar usman da harshensa saboda ku, amam in ki yi fushi ta hanyar amnfani da takubbanku saboda usman! Ku sani usman an kashe shi ne abin zalunta, don haka ku nemi makasansa, idan kun same su to ku kashe su, sannan sai ku sanya lamarin jagoranci shawara a tsakanin mutanen da sarkin muminai dan khaddabi ya zabe su, kuma ba za a sanya wanda ya yi tarayya a jinin usman a cikin su ba.
Masu tarihi suka ce: sai mutane suka yamutse suka sassaba. Da mai cewa: maganar da uwar muminai ta fada haka ne. da mai cewa: me ya hada ta da wannan lamarin bayan an umarce ta da zama gidanta. Sauti ya daga sama, zage-zage suka yi yawa, har sai da aka yi fada da dukan juna da takalma, da jifa da tsakuwa, sannan sai suka ware gida biyu, jama'a tare da usman dan hanif, da wata kuma tare da a'isha da mutanenta.
Tsayawar jama'ar biyu don yaki:
Sai jama'ar biyu ta wayi gari ta yi safu don yaki, usman dan hanif ya fito , sai ya hada a'isha da Allah da musulunci , kuma ya tuna wa dalha da zubair bai'arsu ga Ali. Sai suka ce: mu muna neman jinin usman ne. sai ya ce musu: wannan ai ba sha'anin ku ba ne, ina 'ya'yansa? Ina 'ya'yan ammominsa wadanda suka fi ku cancantar jininsa:? Wallah ba haka ba ne, sai dai ku kun yi hassada ne ga Ali yayin da mutane suka yi ittifaki a kansa, kuma kun yi tsammanin wannan lamarin na jagoranci ya zama a hannunku ne, sai ku yi aiki da shi yadda kuka so, shin akwai wani wanda ya fi kowa tsananta wa usman fiye da ku?!
Sai suka zage shi zagi mai muni, suka kira sunan babarsa da zagi. Sai ya ce da zubair: ba don safiyya ba da matsayin ta gun manzon Allah ba, da ka sani, ka ci albarkacinta ta kai ka zuwa ga inuwa, amma lamarina zai kasance tsakanina da kai ne kai dalha, ya kai dan mace mai wuyar sha'ani wato dalha. Sannan sai ya ce: ya Allah ni na kawo uzuri. Sannan sai ya kai hari sai mutanen suka yi yaki mai tsanani, sannan sai suka rabu suka yi wani shiri na musamman da masu tarihi suka kawo yadda ya kasance dalla-dalla. Suka sanya lamarin ya kasance har sai Imam Ali (a.s) jagoran muminai ya iso basara, kuma jama'ar biyu suka bayar da alkawari ga juna mai karfi da daukar alkawarin Allah mafi tsanani daga abin da wani annabi ya dauka daga alkawarinsa, sannan sai aka sa hannun kan wannan rubutun alkawarin na bangarori biyu.
Sai dai a'isha da dalha da zubari sun ci gaba da aika wa kabilu da sanya labarawa da manyan mutane da masu son mulki da jagoranci da jagororin al'umma wasiku ta yadda shi kansa Imam Ali (a.s) da usman dan hanif da sahabbansa ba su sani ba, yayin da su ma'abota rakumi (jama'ar a'isha) suka gama shirin su sai kawai suka fito a wata rana mai duhun dare da iska da ruwan sama, suna sanye da sulke, da kuma tufafi daga saman sulken, sai suka je masallaci lokacin sallar asuba, kuma usman dan hanif ya riga su zuwa masallacin don ya yi salla, sai ya gabata don yin salla, sai sahabban dalha da zubair suka hana shi, suka gabatar da zubair, sai 'yan sanda suka zo da masu tsaron baitul mali sai suka cire dalha suka gabatar da usman, sannan sai mabiya zubair suak yi galaba kan su suka gabatar da zubair, ba su gushe ba suna hana har sai da rana ta kusa fitowa, sai mutanen da suke cikin masallaci suka yi tsawa cewa ; shin ba za ku ji tsoron Allah ba ya sahabban Muhammad? A lokacin rana ta fito, sai zubair ya yi galaba ya yi salla da mutane.
Yayin da ya gama salla sai ya yi wa sahabbansa masu makami umarni da su kama usman dan hanif. Yayin da suka kama shi sai suka yi masa dukan mutuwa, suka cisge masa gemo da gashin baki, da gira da girar idanuwansa, da dukkan wani gashi da yake kansa ko fuskarsa, suka kuma kama 'yan sanda da masu tsaron baitul mali wurin mutane saba'in daga muminai daga shi'ar Ali suka ta fi da su tare da usmna wurin a'isha, sai ta ce da Abana dan usman dan affan: ka fita da shi waje ka sare wuyansa, ka sani mutanen madina sun kashe babanka. Sai usman dan hanif ya ce: ya ke a'isha da dalha da zubair, dan'uwana sahal shi ne halifa a madina, kuma na rantse da Allah idan aka kashe ni, to sai ya sanya takobi kan 'yan'uwanku da jama'arku kuma babu wani wanda zai bari baki daya. Sai suka kyale shi. Sai a'isha ta yi umarci zubair da ya kashe 'yan sanda da masu tsaron baitul mali baki dayansu ta ce masa: na ji labarin abin da suka yi maka. Sai wallahi zubair ya yanka su baki daya kamar yadda ake yanka tumaki, kuma ya sanya dansa abdullahi a kan yin hakan, su mutane saba'in ne ya yanka su baki daya. Wasu daga cikinsu kuwa suka rage suna masu kare baitul mali suka ce: ba zamu ba ku shi ba, har sai sarkin muminai Ali (a.s) ya zo. Sai zubair ya tafi wuinsu da wasu jama'a daga rundunarsu da dare, sai ya auka musu ya kama ribatattu kusan hamsin daga cikinsu duk ya sare wuyansu baki daya, wannan ne yaudarar da suka yi wa usman dan hanif, wannan ce farkon yaudarar karya alkawarin yaki a musulunci, kuma kashe 'yan sanda da masu tsaron baitul mali shi ne farkon mutanen da suke musulmi a tarihin musulunci da aka kama su aka sare wuyansu haka nan kawai, sun kasance mutane dari da ishirin ke nan, a wata ruwayar cewa sun kasance mutane dari hudu ne (kamar yadda ya zo a shafin na 501, mujalladi na biyu daga sharhin nahajul hamidi).
Sannan sai suka kori usman dan hanif sai ya koma wurin Ali (a.s), yayin da ya gan shi sai ya yi kuka, ya ce masa: na barka ina dattijo, amma na dawo maka ina saurayi maras gemu. Sai Imam Ali (a.s) ya fadi: inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un!. Har sau uku. An jarrabi al'umma da wannan musiba da ba ta hadiyuwa, ya kasance yana kai kukan wannan lamaarin da bakin cikinsa zuwa ga Allah (s.w.t), ya kasance yana fada yana kan mimbari: ya ubangiji ni ina neman taimakon ka kan kuraishawa da wadanda suke taimaka musu, su sun yanke zumuncina, sun kaskanta girman matsayina, sun hadu kan jayayya da ni kan lamarin da yake nawa ne. sannan sai suka ce: ko in karba gisa gaskiya, ko in bar shi bisa gaskiya. Sannan sai ya ambaci ma'abota rakuma ya ce: sai suka fito suna masu jan haramin manzon alahsa kamar yadda ake jan baiwa yayin da za a kai ta kasuwa don sayarwa suna masu fuskantar garin basara, sai suak tsare matansu a gidajensu, suka bayyaar da wacce manzo ya tsare a gida gare su da kuma ga sauran mutanen a rundunar da babu wani mutum daga cikinsu sai dai ya yi mini alkawarin biyayya, kuma ya yi mini bai'a yana mai biyayya ba mai tilastawa ba, sai suka gabatar da wakilina a basra da masu tsaron baitul mali da wasunsu daga mutanen basara, sai suka kashe su haka nan kawai babu wani yaki, wasu kuma suka kashe su da yaudara… haduba ce a nahajul balaga.
Matakin hakim dan jabala :
Yayin da labarin abin da masu rakumi suka yi ya isar wa hakim dan jabala da abin da suka yi da usman dan hanif da masu tsaron baitul mali da wasunsu sai ya fito da mtuaen dari uku daga abdul kais ya kasance shugabansu ne, sai mutanen suka fito don bugawa da shi, sai suka dora a'isha kan wani rakumi, sai wannan ranar aka kira ta da ranar jamal karama, ranar kuma da ta yaki Ali (a.s) da ranar jamala babba.
Sai jama'a biyu suka buga sosai, hakim da mutanensa uska yi yaki mai tsanani, sai dai wani mutum daga azdi sai ya kai hari kan hakim ya sare kafarsa da takobi sai ya yanke ta, sai azdi ya fado daga kan dokinsa, sai hakim ya sunkuya ya dauki kafarsa yankakka ya doki wannan ba'azde da ita, sai ya kayar da shi, sannan sai ya shake shi har sia da ya kashe shi da shakewa har sai da ransa ya fita. Sai wani mutum ya wuce hakim yana daukar rai ya ce masa: wa ye ya yi maka haka? Sai ya ce: matashina wannan. Sai ya duba sai ya ga mutum azdi yana karkashinsa. Hakim ya kasance daga gwarazan larabawa, da masu karfin musulmi, masana da sha'anin biyaya da wilaya ga Ahlul Baiti (a.s). kuma an kashe dansa asharaf a wannan yakin tare da shi da wasu 'yan'uwansa su uku, kuma aka kashe sahabbansa dukkansu tare da shi sun kai kusan mutane dari uku daga abdul kais, dukkansu bayin Allah ne. ko da yake tayiwu wasu daga wadanda aka kashe a ranar daga kabilar bakur dan wa'il ne. yayin da basara ta kasance a hannun a'isha da dalha da zubair bayan kashe hakim da sahabbansa, da kuma kore usman dan hanif daga cikinta, sai aka samu sabani tsakanin dalha da zubair a salla, kowanne yana son ya kasance mai yin limanci ga mutane, kuma yana jin tsoron kada salla bayan dayan ta kasance sallamawa ne gare shi da mika masa wuya, sai a'isha ta yi musu sulhu, ta sanya salla limancin wata rana ga abdullahi dan zubair, wata rana kuma ga Muhammad dan dalha, yayin da suka shiga gidan baitul mali a basara suak ga abin da yake cikinsa na dukiya, sai zubair ya karanta wannan ayar yana mai farin ciki matuka: "Allah ya yi muku alkawarin ganima mai yawa da zaku karbe ta, sai ya gaggauta muku wannan" fathu: 20. Ya ce: mu muka fi cancanta da basara fiye da mutanenta.
Wannan shi ne takaitacce abin da ya faru a basara na lamurra kafin zuwa Imam Ali (a.s) cikinta.
Isuwar Imam Ali (a.s) basara da yakin jama'a biyu:
 Sannan sai Imam al (a.s) ya isa basara da wadanda suke tare da shi, sai a'isha ta tashe tana kare shi daga shiga basara, ta kasance mai ta tsananta kwarai, tana mai fushin zuciya, sai ya kame hannunsa daga yakar ta, ya kuma kame hannayen mutane, yana mai ba su damar su samu sulhu da gyara al'amuran al'umma bisa abin da Allah (s.w.t) da manzonsa (s.a.w) zasu yarda da shi, kuma ya kai matukar neman sulhu da magana da aiki matuka.
Har ibn jarir dabari yana ruwaitowa a tarihi cewa: Ali (a.s) ya kira zubair a wannan ranar sai ya tuna masa wata kalma da annabi (s.a.w) ya fade ta yana ji daga annabi cewa: dan ammarka wannan zai yake ka yana mai zaluntar ka. Sai zubair ya juya ya bar shi, ya ce: ni ba zan yake ka ba. Sai ya koma wurin dansa abdullahi bn zubair ya ce: ba ni da wata basira a wannan yakin. Sai dansa abdullahi ya ce masa: kai ka futo bisa basira, sai dai kai ka ga tutocin dan abu dalib ne kawai, kuma ka san cewa akwai mutuwa karkashinta sai ka ji tsoro. Sai dansa ya dawo da shi da wannan har sai da ma ya kasance yana makyarkyata don fushi, ya ce da dansa abdullahi: kaiconka ni na rantse masa cewa ba zan yake shi ba ai. Sai dansa abdullahi ya ce: ka yi kaffarar rantsuwarka da 'yanta bawanka sarjis. Sai ya 'yata bawan ya mike ya shiga sahun yaki tare da su.
Dabari ya ce: Aliyyu (a.s) ya gaya wa zubair a wannan ranar cewa: kana neman jinin usman guna a yau alhalin kai ka kashe shi, Allah ya sallada wa wanda ya fi tsananta masa daga cikinmu abin da yake ki .
Dabari ya ce: sai ya yi addu'a kan dalha ya ce: ya kai dalha, ka zo da matar manzon Allah (s.a.w) kana mai yin yaki da ita, kana mai boye matarka a gida, amma kai ka yi mini bai'a? sai ya ce: na yi maka bai'a a wuyana akwai tawaye, sai dalha ya dage sai an yi yaki.
A wannan lokacin ne sai Imam Ali (a.s) ya koma zuwa ga sahabbansa ya ce musu: (kamar yadda dabari ya ruwaito): wane ne daga cikinku zai kai musu wannan littafin da neman su yi aiki da abin da yake cikinsa, idan aka yanke hannunsa sia ya rike shi da daya hannun, idan kuma a yanke daya hannun sai ya rike shi da hakorinsa, sai wani saurayi ya ce: ni. Sai Ali ya yi dawafi gun sahabbansa yana neman wanda zai yi hakan, babu wanda ya karba sai wani saurayi. Sai Ali (a.s) ya ce masa: kai musu wannan, ka gaya musu wannan ne zai sulhunta tsakaninmu da ku… har dai zuwa karshe, da hada su da Allah da cewa ku bari mu kame jininmu da jininku. Yayin da wannan saurayin ya zo sai suka kai masa hari a hannunsa akwai littafin sai suka yanke ahnnunsa, sai ya rike shi da harshen sa, sai suka kashe shi. A lokacin ne Imam Ali (a.s) ya ce da sahabbansa: a yanzu kuna da hakkin yakar su, ku yake su.
Babar wannan yaron ta yi masa juyayin abin da ya faru da wasu baitoci kamar yadda dabari ya kawo tana mai cewa :
Babu bakin ciki idan musulmi ya kira su
Yana karanta musu littafin Allah ba ya jin tsoron su
Babarsu tana tsaye tana ganin su
Suna bin bata ba ta hana su
Ta cakuda habar su da jini
Sai mai rakumi ta bayyana don yin yaki, ta riga ta kumburo da fadin kai, kuam yanayin husuma ya taso mata, sai dabi'ar nan ta gabar jahiliyya ta ki ta taso mata, ta kasance ta fi zilubda jur'a da tsaurin kai, ta riga ta ci damarar tufafinta a kan yaki, tana mai hamasa da kuna a cikin rundunarta, sai ta tura su zuwa ga mutuwa a gefen rakuminta, ta duba hagunta sai ta ce: su waye a hagu na? sai sabara dan shiman ya ba ta amsa da cewa: (kamar yadda ya zo a ibn asir) mu ne 'ya'yanki azdawa. Sai ta ce: ya ku alayen gasan ku nuna mana karfin nan naku da muke jin labarin sa a yau, kamar yadda muka ji wani mawaki yana fada:
Da mai karfi (da gogayya) n gasana masu kiyaye ta
Da ka'abu da ausu da shabib duk sun yi gogayya
Azdawa sun kasance suna daukar kashin rakumin suna shinshinawa suna cewa: kashin rakuminn babarmu ya fi almiski kanshi.
Sai ta duba dama ta ce: waye nan damata? Sai suka ce: bakaru dan wa'il ne. sai ta ce: ku nuna mana ranar mawakin nan mai cewa:
Sun zo mana cikin sulken karfe kamar dai su
Su masu izza ne da yakin bakaru dan wa'ili
Tace: ku sani a gaban abdul kais ne suke yaki
Sannan sai ta fuskanci gabanta ta ce: wane mutane ne? sai suka ce: banu najiya. Sai ta ce: madalla, madalla. Takubba ba'abdaha bakuraisha, ku yi gogayya gogayyar masu fansar juna.
Fadin haka sai ya kunna musu wuta kamar an hura wuta mai kuna. Masu tuta a hannunsu suka bi takunkumin rakuminta suna masu mutuwa a gefensa suna cewa:
Ya uwarmu ya matar annabi
Ya matar mai albarka mai shiriyarwa
Mu ne banu dhubba ba ma gudu
Har sai mun ga kawuka suna zuba
Wani jini mai kwarar yana zuba
Ba ta gushe ba tana tayar da hamasar mutanen har sai da aka  soke rakumin bayan an kashe sama da mutane arba'in a kan takumkuminsa, kuma ta samu rushewa da izinin Allah. Kuma ba don taimakon Imam Ali (a.s) ba na kiyaye ta, da tsayawarsa da kansa wurin ganin ya kare ta, da abin da zai faru na fitina mai makanta a wannan yakin ya faru, wannan fitinar da ta kawo rabuwar musulmi har zuwa ranar kiyama, asasin ta ya kasance rikicin siffaini da nahrawan, da kuma karbala, da abin da ya biyo baya har zuwa yau na bala'in falasdin a wannan zamanin namu.
Sai dai dan'uwan annabi (s.a.w) kuma baban jikokinsa ya tsaya kan rakumin ne da kansa, har sai da fitina ta cinye da kanta, sia ya je kusak da dakinta da yake kan rakumi har sai da ya yi kusa da shi –a cikin akwai a'isha- sai ya kai ta wurin inuwa mai kyau sannan sai ya sanya dan'uwanta muhammd don kula da ita da samun wasu salihan mata, kuma ya yi baiwa da ni'ima ta afuwa ga masu yakar sa, ya saki ribatattun yaki daga makiyansa, sannan ya kebanci a'isha da girmamawa da dukkan adin da yad dace da kyawawan halayensa masu daraja, da kuma falalarsa mai game kowa, da hikimarsa mai isa matuka, wannan dukkansa ya zo a littattafan tarihi kamar yadda aka sani.
Kuma ana kiran wannan yakin da yakin jamal babba, ya kasance a ranar alhamis goma ga watan jimada akhira shekara ta talatin da shida, dukkansu bayanansu sun zo a littattafan tarihi. Sai a koma.
Wadanda aka kashe a yakin jamal babba sun kai kusan dubu goma sha uku daga 'ya'yan a'isha a cikinsu akwai dalha da zubair abin takaici, kuma daga moya Ali kusan mutane dubu ko kasa da hakan ko sama da hakan kadan sun yi shahada.
Wannan kuwa duk ya faru alhalin ita uwar muminai ta fi kowa sanin cewa Ali shi ne dan'uwan manzon Allah (s.a.w) kuma waliyyinsa mai gadonsa wasiyyinsa, kuma shi ne wanda Allah da manzonsa suke son sa yake son Allah da manzonsa, kuma shi yana da matsayin haruna ga Musa (a.s) gun manzon rahama (s.a.w), kuma ta ji manzon Allah (s.a.w) yana maimaitawa cewa Allah ya taimaki wanda ya bi shi, ya tabar da wanda ya ki shi, ya taimaki mai taimakonsa, ya tabar da wanda ya ki taimakonsa, da cewa: Allah ya yi rahama ga Ali ya juya gaskiya tare da shi duk inda ya juya.
Kuma ta gani a hajjin bankwana cewa manzon Allah (s.a.w) yana karfafa matsayinsa yana mai umartar al'ummarsa da riko da shi da riko da nauyaya biyu (littafin Allah da alayensa), yana kebantar Ali da wannan shi kadai, yana yi wa al'ummarsa garegadi daga bata idan ba su yi riko da su ba.
Da ranar Gadir da ta ga annabi (s.a.w) ya hau kan mimbari yana yi wa Ali (a.s) wasiyya, yana mai dora shi kan jagorancin al'umma bayansa, tana ji tana gani, a cikin dubunnan jama'a mai yawan gaske a hajjin ban kwana, a daidai inda mararrabar hanya ta raba musulmi zuwa garuruwa.
Kuma ta gan annabin Allah (s.a.w) (ya kalli Ali a fadima da Hasan da Husain) yana mai cewa da su: Ni mai yakar duk wanda ya yake ku ne, kuma amincin duk wanda ya amintar da ku. Kuma duk wannan ahmad dan hambal a masnadinsa  da hakim a sahihinsa na mustadrak da dabarani a littafinsa alkabir, da tirmizi a sanadinsa sahihi zuwa zaid dan arkam duk sun kawo shi, kamar yadda ya zo a tarihin sayyida Zahra (a.s) a littafin isaba.
Haka nan kuma ta gan su yana lullube su da bargo a wannan ranan: yana cewa: ni mai yakar wanda ya yake su ne, mai amintar da wanda ya amintar da su, mai gaba da wanda ya yi gaba da su . Da sauran misalai da suka zo a nassi sahihi wacce ba su boye ba ga a'isha, kai ita ce salkar hadisi da ta ce:  Na hardace hadisai dubu arba'in.
Kuma abin da babanta abubakar ya ruwato ya ishe ta yayin da yake cewa: na ga manzon Allah (s.a.w) ya  sanya wata hema , yana mai jingina a cikin wani baka na larabawak, a cikin hemar kuwa akwai Ali da fadima da Hasan da Husain (a.s), sai ya ce: ya ku mutane, ni mai aminci ne ga wanda ya aminci ma'abota wannan hemar, kuma mai yaki ne ga wanda ya yaki ma'abota wannan hemar, mai son wanda ya jibince su, babu mai son su sai bawa mai arzuta mai halalin haihuwa, kuma babu mai kin su sai bawa shakiyyi tababbe mai mummunan tsatso (dan shege)  .
A yanzu wannan kana ganin a fitowar da a'isha ta yi tana nufin Allah da manzonsa da gidan lahira ne, kuma ita tana daga masu kyautatawa daga mata na gari? Kuma duk wannan tana neman ladan da Allah ya yi wa matan annabi alkawarinsa ne yayin da yake cewa: Kuma idan kuna son alla da manzonsa da ranar lahira to Allah ya tanadar wa masu kyautatawa daga cikinku lada mai girma. Ahzab: 29.
Ko kuma tana da wata dangantaka da Allah ne da zata halasta haram dinsa a kan dukkan talikai? Don haka sai ta yi abin da ta yi na fita kan Imami (a.s) tana mai samun nutsuwa da amintuwa daga azabar Allah yayin da yake cewa: ya ku matan annabi wacce ta zo da wani alfahasha bayyananniya daga cikinku, to za a ninka mata azaba ninki biyu, kuma wannan abu ne mai sauki wurin Allah. Ahzab: 30.
Ko kuma kana ganin fitar ta wannan ibada ce ga Allah da rusunawa ga umarnin Allah da manzonsa da aiki na gari? Sai ta zabe shi a matsayin aiki da fadin Allah madaukaki da cewa: wacce ta yi biyayya daga cikinku ga Allah da manzosa kuma ta yi aiki na gari za a ba ta ladanta kashi biyu, kuma mun tanadar mata da arziki mai girma. Ahzab: 31.
Ko kuwa tana nufin ta nuna takawa da tsentseni ne da fitarta ban da sauran matan annabi (s.a.w), don ta fifice su da yin aiki na gari da aiki da fadinsa madaukaki: ya ku matan annabi ba kamar sauran mata kuke ba idan kuka yi takawa. Ahzab: 32.
Shin ta ga dakin ibn dhabba shi ne dakin da Allah ya yi umarni ta kasance cikinsa yayin da yake cewa: kuma ku tabbata a gidajenku kada ku yi fita irin fitar jahiliyyar farko, kuma ku tsayar da salla, ku bayar da zakka, ku bi Allah da manzonsa. Ahzab: 33.
Me za ta ce? Ko me masoyanta suke cewa: a fadin da Allah ya yi mata magana ita da sahibarta (Hafsa): Idan kuka tuba ai dai zuciyarku ta rika ta karkace , kuma idan kuka tarar masa, to Allah shi ne majibinsa, da jibrilu da salihul muminin, da mala'iku su ma suna goyon bayansa . Kuma idan ya sake ku, to ubangijinsa zai canja masa da wasu mata da suka fi ku, musulmi, muminai, masu ibada. Tahrim: 4 – 5.
Kuma wannan ya ishe su hujja gun Allah, misalin sa mai girma ne wanda Allah ya nuna musu su biyu a surar tahrim; a fadinsa madaukaki: Allah ya sanya misalin wadannan da suak kafirta matar Nuhu da matar Ludu, sun kasance a karkashin bayinsa biyu na gari, sai suka ha'ince su, kuma ba su wadatar da su komai ba daga Allah, kuma aka ce da su ku shiga wuta tare da masu shiga. Kuam Allah ya buga misali da wadannan da suka yi imani matar fir'auna yayin da ta ce ubangiji ka gina mini gida gun ka, ka tserata da ni daga fir'auna da aikinsa, ka tseratar da ni daga mutane azzlumai. Tahrim: 10 – 11.
Labarin ta isa mamaki kan abubuwan da ta yi tana mai kiyayya da Ahlul Baiti da a aikace yayin da mawakin yake cewa:
Ya ke a'isha me za mu ce game da yakar ki
Kin shiga mashigar halake – halake
Ya ishe ki abin da buhari ya kawo
A sahihin littafinsa na nuna dakinki
An ce kin tuba Ali yana abin kashewa
To me ya kika yi sujadar godiya yayin da ya rasu
Kuma me ya sa kika hau alfadari ranar Hasan
Kina hura wutar wadancan fitintinu

tarjamar; Hafiz Muhammad: hfazah@yahoo.com