Ilimin Gaibi



 Shin Akwai Wanda Ya San Gaibi Ban Da Allah?

Idan muka duba ayoyin Kur'ani mai girma zamu ga suna nuna mana sanin gaibi da ma abin da yake sarari duk na Allah ne; ayoyi kamar: Naml: 65, da An’am: 59. Sai dai idan mun lura zamu ga sanin gaibi da ma'anar da ya zo a wannan ayoyin bai kore samuwar saninsa ga wasu bayi da Allah ya zaba ba, don haka ne zamu iya fahimtar ma'anar babu wanda ya san gaibi sai Allah tana nufin asalin saninsa, da cewa; babu wanda ya san gaibi da kansa sai ubangiji madaukaki. Amma wanin ubangiji idan ya san gaibi to da sanarwar ubangiji ne ba da kansa ba, don haka saninsa da gaibi yana bin sanarwar da Allah ya yi masa ne, da ba shi kyautar wannan ilimi da Ubangiji madaukaki ya yi, don haka ne zamu ga ayar nan ta surar Jinn: 26-28, da sauran ayoyi kamar: Aali Imran: 179, 44, da Yusuf: 102, duk suna nuni da haka.

A cikin Kur'ani mai girma ya zo da bayanin annabawa (a.s) da Allah madaukaki ya sanar da su gaibi, idan mun koma wa ayoyi kamar haka: Yusuf: 41, da Aali Imran: 49, zamu ga yadda annabawa suka san gaibi kuma suka gaya wa mutane shi. Kamar yadda zamu samu labarun fadin abubuwan da zasu wakana da imam Ali (a.s) da sauran imamai (a.s) suka yi, kamar yadda ya zo a cikin Nahajul Balaga: 186, An’am: 75, da Kafi: 1/257. Sai dai sun sanar da mutane cewa; wannan duk daga koyarwar manzon Allah (s.a.w) da ya sanar da su, wato; ba sun sani ba ne su a kashin kansu, sai dai sanarwa ce daga Allah da manzonsa.

Hafiz muhamad Sa'id

Thursday, September 24, 2009

 



back 1 next