Shirin Salla



 

Shirin salla:

Ya mike tsaye yanamai fuskantar alkibla, sa’annan sai ya yikiran salla bayan nan yayi Ikama, wannan shi ne aikinda zai yikafin kabbarar harama a kowace salla daga sallolibiyar na wajibi  wato Asuba da Azaharda La’asar da Magriba daIsha’I.

Bayan Kiran sallah da Ikama saiya tayar da kabbarar haramadomin shiga cikin salla dafara ayyukan salla yanamai fadin kalmar (AllahuAkbar)

Sa’annan ya karantasurar Fatiha kamar haka :

بِسْمِ اللهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْمِ، الْحَمْدُ ِللهِ رَبِّ الْعَالَمِيْنَ، الرَّحْمَنِ الرَّحِيْمِ، مَالِكِ يَوْمِ الدِّيْنِ، إيَّاكَ نَعْبُدُ وَ إيَّاكَ نَسْتَعِيْنُ، اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيْمَ، صِرَاطَ الَّذِيْنَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ الْمَغْضُوْبِ عَلَيْهِمْ وَلاَ الضَّالِّيْنَ

(Bismillahirrahmanirrahim ▪ Alhamdulillahi rabbil ‘Alamin ▪ Arrahmanirrahim▪ Maliki yaumiddin▪ Iyyaka na’budu wa iyyaka nasta’in▪ Ihdinas siratal mustakim ▪ Siratal lazina an’amta ‘alaihim gairil magdhubi ‘alaihim waladh dhalin)

Sa’annan sai yakaranta wata sura kamar SuratulAhad.

بِسْمِ اللهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم،ِ قُلْ هُوَ اللهُ أَحَدٌ، اللهُ الصَّمَدُ، لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُوْلَدْ، وَ لَمْ يَكُنْ لَهُ كُفُوًا أَحَدٌ



1 2 3 4 5 6 next