Gwagwarmayar Musulmi



 

Gwagwarmayar Musulmin Duniya

Muhimmancin sanin siyasar musulunci ya girmama ta yadda zamu ga musuluncin ya k'i tsayuwa sai da wannan lamarin na siyasarsa, kuma hatta da kalmar shahada tana k'ark'ashin bayanin siyasar musulunci ne yayin da take nuna mana waye za a yi wa d'a'a da biyayya, zuwa ga wa za a mik'a wuya gaba d'aya.

Don haka ne zamu ga karkacewar duniyar musulunci da durk'ufewarsu da rushewarsu ta samu asali ne daga kaucewa siyasar musulunci da amsa kira sab'anin wasiyyar annabi (s.a.w) da ya yi musu wasiyya da halifofinsa goma sha biyu.

A wannan zamin an samu yunk'uri daga malamai masana na dukkan b'angarorin mazhabobin musulmi domin ganin an samu canji bayan rushe daulolin musulmi da 'yan mulkin mallaka suka yi a k'arnin da ya gabata, muna ganin yadda masana kamar sayydi K'utub da Shahid Sadar suka yi rubutu kan Daular musulunci[1]. Sayyid K'utub a matsayinsa na fuskar gwagwarmayar 'yan'uwa musulmi yana ganin cewa: Al'umma ta kaucewa kalmar shahada ne sakamakon rashin fahimtar ma'anar kalmar shahada da kawar da shari'ar Allah a gefe guda, sannan sai aka samu yankewar al'umma da rarrabarta, sai muka koma rayuwar jahiliyyar zamani, kuma babu wata hanyar fita daga wannan duhun kafircin na jahiliyya sai ta hanyar komawa da sake rungumar musulunci, sai a samu kalmar shahada mai d'auke da jagorancin shari'ar musulunci da hukumarsa a matsayinsa na rukuni na asasi daga rukunonin kalmar shahada, kuma dole ne a fuskanci wannan lamarin da yak'i da jihadi kamar yadda al'ummar farko ta yi domin kawar da duk wani shinge da ya kange isa zuwa ga hadafin kama daular musulunci. Yana ganin mas'alar ijtihadi mas'ala ce mai sauk'i, kuma ana iya samun amfanuwa da kowane littafin fik'ihu domin cimma hadafin.

Amma babban malamin na ta tafarkin mazhabin Ahlul Bait (a.s) shahid Sadar yana ganin cewa; Wannan al'ummar ta musulmi tana kan wata hanya ce ta neman samun kamala domin saduwa da Allah mad'aukaki, kuma wannan tafarki ne mai nisa matuk'a da zai ci gaba domin samun kaiwa zuwa ga mafi girman mai misalta Ubangiji a duniya, kuma a wannan tafiya ne masu son ganin sun bice wannan haske suke kange hanyar ma'abota neman wannan kamala, masu kange wannan hanyar ta kamala sun had'a da miyagun malamai masu hana shiriya isa zuwa ga mutane da azzaluman masu mulki daga wad'anda suke munana ayyuka suna tsammanin suna kyautata ayyuka.

Don haka mas'alar ba ta tak'aita da batun shelanta juyi ba ko jaddada kalmar shahada tun asali, ko kafirta al'ummar musulmi, wannan mas'alar ta shafi lamarin ci gaba zuwa ga Allah ne, kuma babu wani k'aidi da dabaibayi a cikin wannan tafiya mai d'auke da Asasin ak'ida guda biyar: wad'annan asasin sun had'a da Kad'aita Allah, da Annabci, da Imamanci, da Adalci, da Makoma, wannan lamari ne da sayyid K'utub bai yi maganarsa ba domin abin da ya fi shiga gabansa shi ne batun d'abbak'a shari'ar musulunci a cikin al'umma, don haka ne ma juyin juya hali a mahangarsa yake abu ne tauyayye, domin bai kula da janibin mai misalta Allah a bayan k'asa ba, bai waiwayi asasin imani da keb'antacciyar ma’anarsa ba, ya k'arfafi abin da ya shafi d'abbak'a hukuncin Allah a bayan k'asa ne, don haka ne ma muna iya ganin wad'anann juyin da suka samu tunaninsu da madogararsu daga tunaninsa ta tuk'e zuwa ga inda take a yau.

Kawar da batun mas'alar kyakkyawan misalin da yake almata addinin Allah a duniya da sayyid K'utub yake da shi ya taso ne daga nau'in tunanin mazhabinsa, wannan lamarin ya kai ga sandarewar motsi wuri d'aya, sai ya kasance ya dogara bisa taken kiran d'abbaka hukuncin Allah, a lokaci guda kuma ya manta da jigon tafiya wanda yake shi ne misalin kamalar d'an Adam a duniya, kuma wakilcin Allah mai muhimmanci a duniya.

Abin da shahid Sadar ya yi nuni da shi yana da muhimmanci matuk'a, muna ganin tun ranar da manzon rahama ya bar wannan al'umma ta samu kanta a cikin sakacin barin wannan janibi da yin tutsu da shi, wannan lamarin ne ya kai ta zuwa ga inda take a yau na rashin mafita a lamurranta, kuma ya kai ta ga jahiltar ma'anar shi kansa addini kamar yadda Allah ya saukar da shi, ya kai ta ga d'imaucewa da rarraba, kuma ba ta da wata mafita sai komawa zuwa ga misali mai girma na mutum mai cikakkiyar kamala. Wannan mutumin shi ne tafarkinsa zai iya kama hannayenta zuwa ga tsira da shiriya, zuwa ga ilimi da hikima, zuwa ga haske da rabauta. Shi ne abin da dukkan magabatan jagororin Ahlul Baiti (a.s) suka aiwatar, motsin Imam Ali da Hasan da Husain (a.s) bai kasance ba sai don wannan hadafin, kuma rashin masu taimakawa ga wannan hadafin ya sanya komai an ajiye shi ba a mahallinsa ba, sai ga mimbarorin Annabi babu mai hawa sai wanda Annabi (s.a.w) ya yi fushi da shi, babu wani abu da ya rage wa musulunci sai suna, Kur'ani kuwa babu abin da ya rage masa sai rubutun.

Masu hana hanyar Allah da fashin imani sun yi k'ok'arin ganin sun cimma burinsu ta dukkan hanyoyin da ba su dace ba: An bayar da rashawa, da alk'awarin mak'amai, da kisa, da yaudarar siyasa, da kai hari da mamayar garuruwa, da kashe yara da mata, da halatta jini da tsoratarwa, da keta mutunci da talautarwa, mutane ne da suka k'i Muhammad da alayen Muhammad, sannan kuma yawancin al'ummar musulmi yayin da take maganar shari'a sai ka ga ta samu daga irin wad'annan daulolin ne.

Sai irin wad'annan ma'abota waccan karkatacciyar shari'ar suka yi munanan abubuwan da suka kawar da kamannin musulunci daga asalinsa, mafi munin abubuwan da suka yi sun kasance duka ne ga musulunci da har yau aka kasa gyara shi; sun halatta haram, sun haramta halal, sun halatta cin riba da kud'in ruwa, sun jingina wasu mutane zuwa ga wanin iyayensu, kai an kashe sahabban manzo da sauran bayi nagari, aka la'anci alayen Annabi (a.s) a kan mimbarori, aka d'aga matsayin masu gaba da su, aka k'irk'iro hadisan k'arya don kambama masu gaba da alayen Annabi (s.a.w) sannan kuma aka yi k'ok'arin ganin kawar da falala da fifikon alayen Muhammad (a.s), aka kuma bi mabiyansu da kisa da k'ararwa, sannan sai aka mik'a mulki da jagoranci hannun mutane irin su Yazid, suka halatta Makka da Madina, sannan suka kashe jikokin manzon Allah (s.a.w). Daga baya kuma sai ga malaman fada sun kama aiki dare da rana babu k'ak'k'autawa, sai suka shiga cikin karkatar da tarihi da yabo ga dukkan masu k'iyayya da gaskiya, sun jirkita tarihin al'umma, hatta da Imam Husain (a.s) da aka kashe domin ganin tsayar da kyakkyawa da hani ga mummuna da tsayar da adalci da kuma gina al'umma domin ta samu kamalar da Allah yake son ta samu sai da aka jirkita lamurransa da cewa don neman halifanci ne kawai.

Imam Ali (a.s) da d'ansa Imam Husain (a.s) sun yi addu'o'i a kan wannan al'umma da d'imuwa kuma haka nan zamu ga wannan al'umma ta ci gaba a kan hakan har yau d'in nan, babu wani wanda yake tambayar dalilin wannan d'imuwar balle ya shiga neman amsarta. Ubangiji kuwa ba ya ba wa al'umma dama sau d'ari, kai ko sau goma ma, kai ko sau uku ma, don haka wannan al'ummar tamu ta yi asarar dama masu yawa da samu ba ta yi rik'o da su ba, sai ta ci gaba har zuwa wannan rana tamu cikin d'imaucewa, irin wad'annan damar suna zuwa ne a wasu lokuta tak'aitattu 'yan kad'an, al'umma ce da ta samu damar Imam Ali da Hasan da Husain (a.s) amma sai ta watsar da damar. Don haka ne sai dare ya lullub'e ta da duhunsa, zalunci ya mamaye ta da hannayensa, jahilci ya kame ta tun daga kanta har k'afafunta, wannan duhu ne da babu mai iya yaye shi sai Imam Mahadi (a.s) Allah ya gaggauta bayyanarsa. Hak'ik'a an jarraba dukkan nau'in mulki a kan wannan al'ummar in banda adalci, an jarraba Umayyanci, da Abbasanci, da Usmananci, an jarraba gurguzu da demakrad'iyya, an zubar da jini, an haifar da yak'ok'i da rikici, adalci ya yi k'aranci, abin takaici duk wannan an yi shi da sunan musulunci! Kowanne yana kisa da zato, yana halatta giyoyi, yana keta alfarma, kai sai ga daga k'arshe hukuma ta kai hannun 'yan babu ruwanmu da addini, da 'yan k'asanci da gurguzu, da mulkin danniyar gadon sarauta, kai an jarraba komai a kan wannan al'umma in ban da adalci.



1 2 next