Sanawiyya



Sanawiyya

Wannan Hadisi ruwaya ce daga Sadiku Ahlil Bait (A.S) game da tattaunawar Manzo da Ma'abota wannan addini wanda a cikinsa akwai usulubi mai kyau na muhawara da ma'abocin wata Akida da ta saba ta da mai muhawara, wanda a cikinta zamu koyi muhawara da mukabala da munazara da hanyar da take mafi kyau kamar yadda aka yi umarni da (Bil lati Hiya Ahsan). Yana kuma koyar da Hanyoyin kafa dalili Mubashir wato dalili na kai tsaye da kuma Gaira mubashir, da kuma Jawabil halli wato Hanyar warwara da kuma Jawabin Nakdi, wato Hanyar kama mutum da abin da ya yarda ya kuma yi imani da shi. A lokaci guda kuma yana iya nuna mana hakikanin manufar wannan Addini da yadda ma’abotansa suke fassara Akidojinsa. Kuma tana nuna mana yadda aka canja koyarwar Addinin da ya gabata, al'amarin da wannan al'umma ba ta tsira daga irinsa ba ta hanyar riko da Raunanan maganganu ko kuma Tafsirin da ya kafu bisa mahanga ta kuskure da yakan kai ga kurakarai wajan fahimtar Addinin Allah.

Da yake mutane a kowane zamani hali daya ne da su, al’ummar karshe ta Manzon Allah (S.A.W) ma ba ta fita daga irin wannan ba, shi ya sa aka samu sabani da ya kai su zuwa ga rarraba zuwa Mazhabobi da Kungiyoyi na Akida daban daban. Amma wani abin da za a gode wa Allah shi ne al’ummar nan ta bambanta da sauran al’ummu, domin su wadancan al’ummu bayan sun yi nesa da Wasiyyan Annabawan sukan kuma yi rashin sa’ar canza Addinin nasu gaba daya a kuma kautar da Akidunsu daga sahihancinta kamar Yahudawa da Kiristoci da Zartush da Sa’ibawa da sauransu. Amma wannan al’umma Allah ya yi alkawarin kare littafinta, shi ya sa ma duk wanda yake ganin wani yana da Alkur’ani daban da wanda yake hannun musulmi to yana ganin Allah Ajizi ne daga alkwarin da ya dauka na kare littafinsa, kuma irin wadannan mutane suna a matsayin wadanda suka kafirce wa Allah ta hanyar kafircewa Ayar Alkur’ani mai girma.

`MUNAZARAR MANZO (S.A.W)

Imam Assadik (A.S) ya ce: "Daga Babana Albakir (A.S) daga Kakana Ali Dan Al-Husain (A.S) daga Babansa Husain Shugaban Shahidai (A.S) daga Babansa Ali Dan Abi Dalib (A.S) cewa, wata rana ma’abota Addinai biyar suka hadu a wajan Manzon Allah (S.A.W); Yahudawa da Kiristoci da Dahariyya da Sanawiyya da Mushrikan larabawa.

Sai Yahudawa suka ce: Ya Muhammad! Mu muna cewa: Uzairu (A.S) dan Allah ne, mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu to mun riga ka shiryuwa zuwa ga gaskiya, amma idan ka saba mana zamu yi jayayya da kai. Kiristoci suka ce: Mu muna cewa Isa (A.S) dan Allah ne da ya shiga cikinsa ya hade da shi idan ka bi mu mun riga ka zuwa ga gaskiya amma idan ka saba to ma ja da kai . Dahariyya suka ce: Ya Muhammad! mu muna cewa: Halittu ba su da farko ba su da karshe suna nan har abada, kuma mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu mun riga ka fahimtar gaskiya idan kuma ka saba mana to ma ja da kai. Sanawiyya suka ce: Ya Muhammad! mu muna cewa haske da duhu su ne masu juya dukkan ala’amura, mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu to mun riga ka fahimtar gaskiya amma idan ka saba mana ma ja da kai. Mushrikan larabawa suka ce: Ya Muhammad! Mu muna cewa: Gumaka Ubangizai ne, mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu mu mun fika mun riga ka zuwa ga gaskiya da shiriya amma idan ka saba mana to ma ja da kai.

Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Na yi imani da Allah daya ba shi da abokin tarayya, na kuma kafirce wa duk wani abin bauta ba shi ba. Sannan ya ce Allah (S.W.T) ya aiko ni zuwa ga mutane gaba daya Mai albishir da gargadi ga mutane sannan zai mayar da kaidin duk mai kaidi kansa.

SANAWIYYA

Sa’annan sai Manzo (S.A.W) ya fuskanci Sanawiyya da suka ce: Haske da Duhu sune masu tafiyar da al’amuran rayuwar halittu, ya ce:Menene ya kai ku ga fadin haka? Sai suka ce: Saboda mun samu Duniya kala biyu akwai Sharri da khairi, muka kuma sami Al-Khairi yana kishiyantar Sharri, saboda haka sai muka yi musun ya zama mai aikata wadannan abubuwa ya zama daya da yake aikata abu sannan ya zo da kishiyarsa, don haka dole ne ya zama kowanne yana da mai aikata shi, shin baka ganin cewa mustahili ne kankara ta kona ruwa kamar yadda  ba yadda zai yiwu wuta ta sanyaya ruwa!? Don haka ne muka tabbatar da cewa akwai Dadaddu biyu Masu kagowa ga Duhu da Haske.

Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Shin ba kwa ganin Baki da Fari da Ja da Yalo da Kore da Bulu , kowanne yana kishiyantar juna, domin mustahili ne guda biyu daga cikinsu su hadu waje daya kamar yadda zafi da sanyi kishiyoyi biyu ne da mustahili ne su hadu waje daya? Suka ce: Na’am. Ya ce: Don me ba ku tabbatar da Kadimai da adadin launinsu ba, ku sanya wa kowanne daga cikin kishiyoyin nan Kadimi mai yin sa da ya zama ba mai yin dayan ba?. Sai suka yi shiru. Sannan ya ce: Yaya a ka yi Haske da Duhu su ka cakuda, alhalin wannan sha’aninsa shi ne ya yi sama wancan kuma ya yi kasa!?. Shin kuna ganin da wani mutum ya yi Gabas yana mai tafiya wani kuma ya yi Yamma yana mai tafiya a ganinku zai yiwu su hadu? Suka ce: A’a. Sai ya ce: Ashe kenan dole ne kada su Hasken da Duhun su hadu, domin kowanne ya fuskanci fuskar da dayan bai fuskanta ba!. Yaya aka yi kuka samu faruwar haduwar wannan Duniya daga abubuwan da suke bai yiwuwa su hadu? Hakika su dai ababan juyawa ne ababan halitta. Sai suka ce: Zamu duba al’amarinmu.

 Imam Assadik (A.S) ya ce: Sai suka ce : “Zamu duba al’amarinmu”. ya ce: “Na rantse da wanda ya aiko shi (S.A.W) da gaskiya kwana uku bai yi musu ba sai da suka zo wajan Manzon Allah (S.A.W) suka musulunta, sun kasance mutane ishirin da biyar ne; Biyar daga kowace Kungiya. Suka ce: Ya Muhammad! Ba mu ga Mai dalili kamar naka ba, mun shaida kai Manzon Allah ne!!.”

Hafizu Muhammad Sa’id Kano Nigeria

GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKA.

 



1 next