Dahariyya



Ya ce da su kuma: Idan wannan bangaren da sashensa yake bukatar sashe domin ya yi karfi ya cika shi ma Dadadde ne to ku bani labari da ya kasance Fararre da yaya ya kamata ya kasance? kuma yaya siffarsa ya kamata ta kasance?.

Imam Assadik ya ce: Sai suka dimauce suka san cewa ba yadda za a yi a samu Fararre da sifa da suke siffanta shi da ita sai sun same ta ga wannan abin da suka raya cewa Kadimi (Dadadde) ne. Saboda haka sai suka tage suka ce: Zamu duba al’amarinmu tukuna.

Imam Assadik (A.S) ya ce: Sai suka ce : “Zamu duba al’amarinmu”. ya ce: “Na rantse da wanda ya aiko shi (S.A.W) da gaskiya kwana uku bai yi musu ba sai da suka zo wajan Manzon Allah (S.A.W) suka musulunta, sun kasance mutane ishirin da biyar ne; Biyar daga kowace Kungiya. Suka ce: Ya Muhammad! Ba mu ga Mai dalili kamar naka ba, mun shaida kai Manzon Allah ne!!.”

Hafizu Muhammad Sa’id Kano Nigeria

GODIYA TA TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI.

 



back 1 next