Sayyid Khomaini



Ranar talata, biyar ga watan Yunin nan ne ya dace da kewayowar shekaru goma sha takwas da wafatin Imam Ayatullah Ruhullah al-Musawi al-Khumaini, ja-goran juyin-juya-halin kasar Iran. Imam Khumaini (Allah Ya girmama matsayinsa) ya koma ga Mahaliccinsa ne a ranar 5/5/1989, bayan ya gabatar da wasu manyan hidindimu da miliyoyin mutane ke dauka a matsayin gudunmawa ga addinin Musulunci da dan Adam baki daya.

Tunawa da wannan babban mutum a irin mummunan halin da duniyar dan Adam da kasashen Musulmi suke ciki a yau ya zama dole; wannan kuwa saboda nazari a kan abubuwan da ya shimfida ne a fagagen karantarwarsa da ayyukansa, wadanda suke kunshe da magungunan matsalolin al'umma da wadanda ake zalunta a duniya baki daya.

Duniya ta san Khumaini ne da juyin-juya halin da ya ja-goranta, wanda ya haifar da gwamnatin Musulunci a kasar Iran, abin da ya kawo karshen tsohon matsayin da kasar ke kai na zama sansanin hukumomin leken asirin kasashen Ingila da Amurka da Isra'ila, da kasancewa cibiyar aiwatar da muradun 'yan mulkin-mallaka masu wawure dukiyoyin al'ummu masamman a yankin gabas ta tsakiya mai tarin arzikin bakin gwal (man fetur). Manazarta da masu bin diddigin lamurra sun fi mayar da hankali a kan wannan bangare na tarihin wannan babban mutum, ba tare da kulawa da abubuwan da suka kewaye rayuwarsa kuma suka yi tasiri a kan kudurorinsa da matakan da ya rika dauka ba. Wannan ya sa na fahimci mahimmancin rubuta wani abu -komai kasawarsa- a kan bangarorin da suka share fagen wancan babban aiki da kowa ke iya ganinsa daga rayuwar Imam Khumaini, don masu karatu su san cewa ba haka kawai abubuwan da suka haifar da irin kafiyar Imam da kangarewarsa ga manyan 'yan kama-karya na duniya da shimfida kakkarfar gwamnatin Musulunci da ta ci gaba da wanzuwa a kan wannan tafarki na 'yanci da dogaro da kai da ya kirkira suka kasance ba. Maimakon haka nagartaccen shiri da karfafan asasai na Musulunci ne suka samar da irin wannan Mujaddadi da ya sauya tafiyar duniya da tunanin miliyoyin jama'a a karni na ashirin/ashirin da daya; karnin ilimi da wayewa, karnin bunkasar kimiyya da fasaha.

A Matsayin Dalibi

Imam Kumaini bai yi wa ayyukan addini shigan-burtu ba, sai da ya tanaji kansa a ilmance da tarbiyya. Kai! a sama da shekaru tamanin din da Imam ya share yana ayyukan addini, gwagwarmayar kafa gwamnatin Musulunci ba ta lashe kashi daya bisa ukun shekarun ba! Domin ya fara wannan aiki ne kai tsaye a shekara ta 1963; ka ga idan aka lissafa haka zuwa shekarar da ya rasu (1989) za mu ga shekaru ashirin da shida ya share yana harkokin siyasa da gwamnati. Wannan na nufin ya share kusan shekaru sittin yana harkokin ilimi -tarbiyya da karatu da karantarwa. Babu mamaki nasarar da ya samu ta kai yadda muke shaida ta a yau!

Da farko dai Imam dan malamai ne kuma jikan malamai. Kuma gidansu ya shahara tuntuni da ilimi da takawa da jihadi. Mahaifinsa shi ne Ayatullahi Sayyid Mustafa al-Musawi, ya kasance Mujtahidi (wanda ya kai kololuwa a ilimin furu'a ta yadda ba ya bukatar fatawa daga wani malami sai dai shi ya bayar). Mahaifiyarsa, Sayyida Hajara, 'yar gidan malamai ce; domin jika take ga marigayi Ayatullahi al-Khunsari, ma'abucin manyan talife talife a fannonin Musulunci masu yawa. Wannan ne ya share wa Imam fagen shiga fagen karatun addini don zama abin da ya zama a fannonin ilimi.

Tun yana karami ya fara karatuttukan share fage da suka shahara a cibiyoyin karatun addini na lokacin, wato Adabin Larabci (ilimin lakantar harshen larabci) da Mandiki (ilimin lakantar hanyoyin sahihin tunani) da Fikihu da Usulul-Fikih a hannun manyan malaman garinsu -Khumain. Ya fara karatunsa ne a hannun babban wansa Ayatullahi Sayyid Murtadha Basandideh al-Khumaini (saboda ya tashi maraya ne). Ban da shi kuma ya yi karatu a hannun malamai irin su Mirza Mahmud Iftikharul-Ulama, da Mirza Ridha al-Najafi al-Khumaini, da Sheikh Ali Muhammad al-Burjurdi, da Sheikh Muhammad al-Gholpegani, da Sheikh Abbas al-Araki. A shekara ta 1919 ne ya yi hijrarsa ta farko zuwa Arak don ci gaba da karatunsa a lokacin yana da shekaru goma sha bakawai da haihuwa. Bayan shekaru uku (a shekara ta 1922) ya tafi birnin Kum, inda saboda kaifin hazakarsa da kwazonsa ya share marhalolin kammala karatu da sauri irin na ban mamaki. A cibiyar ilimi ta Kum ya yi karatu a hannun manyan malamai irinsu Sheikh Mirza Muhammad Ali Adib, da Ayatullahi Sayyid Muhammad Taki al-Khunsari, da Ayatullahi Sayyid Ali al-Yathribi al-Kashani. Ya kuma yi karatun Furu'a mai zurfi a hannun shuganan Cibiyar Ilimi ta Kum na lokacin, wato Ayatullahi Abdul-Karim al-Ha'iri.

Imam bai takaita da ilmummukan da aka saba kwarewa a kansu a cibiyoyin ilimin addini na lokacinsa ba, kwadayinsa ga ilimi sun sa shi ya zurfafa karatun wasu darussa na gefe (a bisa tsarin lokacin) irin su Falsafa, wadda ya karanta ta a hannun Sayyid Abul-Hassan al-Rafi'i al-Kazwini. Haka ya karanta Irfani (Sufanci) a hannun Sheikh Mirza Ali Akbar al-Hakimi al-Yazdi. Ya karanta Aruli da Kafiyya (ilimin lakantar waken larabci) a wajen Sheikh Muhammad Ridha Masjid Shahi al-Isfahani; haka a wajen wannan malami ne dai Imam ya karanta Falsafar Musulunci da Falsafar Turawan Yamma. Sannan ya zurfafa ilimin da Irfani (Sufanci) na nazariyya a wajen Ayatullahi al-Haj Mirza Jawad al-Malaki al-Tabrizi. Bayan nan Imam ya share tsawon shekaru shida yana karantun Tarbiyya (Irfani na aikace) a hannun Ayatullahi Mirza Muhammad Ali Shah Abadi. Wannan malamin na karshe ya yi matukar tasiri a rayuwar Imam na tarbiyya, ta yadda ya rika yawan ambatonsa da yi masa addu'a a talife talifensa da zantukansa.

Cikin dan lokaci sai da Imam ya zama majingina a ilimi, saboda kwarewar da ya yi a fannonin Fikihu da Usulul-Fikh ta yadda sai da ya kai matakin ilimi na ijtihadi (ikon fitar da hukunce hukunce daga tushensu na asali) a lokacin samartakarsa, ban da kwarewa da ya yi a sauran fannonin ilimi da ambatonsu ya gabata. Wannan ya sa ya yi rata wa malaman zamaninsa, wadanda suka saba kwarewa a wani fanni (masamman na Fikihu da Usulul-Fikh) tare da sassauci a kan sauran bangarorin (masamman na Falsafa da ilumman hankali).

Wannan takaitaccen bayani kan rayuwar Imam ta dalibta ya nuna irin nisan da ya yi a gogayya da ilimi da malamai da yalwar iliminsa, wadanda su suka fi tasiri a ayyukan da ya gabatar daga baya na karantarwa da tarbiyya da jihadi da gwagwarmayar siyasa.

Malami Na Allah

Imam Khumaini (Kuddisa Sirruhu) ya bayar da kyakkyawan misalin nagartaccen malami. Yi masa kyakkyawar fahimta zai taimaka mana wajen riskar abin da ake ruwaitowa daga Manzo [SAWA] mai cewa: "Malamai magadan Annabawa ne." AlKur'ani kuwa ya bayyana ayyukan Annabawa da cewa shi ne "Tsarkakewa da Karantarwa." Imam ya aikata ilimi kwarai da gaske. Ya guji duniya da abin da ta kunsa na kyale-kyale, ta yadda har ya bar duniya a gidan haya yake zaune; bai mallaki gidan kansa ba (sai na gado da ya yi tarayya da 'yan'uwansa a kai). Haka bai damu da kyale kyale irin na sutura da motocin alfahari ba (bai ma taba mallakar motar kansa ba). Ya yi matukar tarbiyyar kansa ta yadda sai da masu kallonsa suka rika shaida siffofin kamala a tare da shi, masu sauraron zantukansa suka rika hakaito zubar hikima daga bakinsa, masu zama da shi suka wa'azantu daga dabi'unsa, har wasu sukan zubar da hawaye da ganinsa, saboda yadda yake tuna musu Allah Madaukaki.



1 2 next