Adalcin Samuwar Mahadi



Adalcin Allah Da Samuwar Imam Mahadi (A.S)

Hakika kowane juyi yana bukatar gabatarwa, da sharudda na fikira da tunani, muna iya sanya rashin yardar mutane a dukkan duniya daga zaluncin da ya yadu a cikinta na azzaluman dauloli da kuma neman al’umma ga samar da adalci da sulhu a duniya ta wani bangaren a matsayin abubuwan na dole masu share fage domin samuwar juyin juya halin duniya na imam Mahadi (A.S).

Na Daya- Share Fagen Fikirar Hakikar Juyin Adalci

Abin da zai wakana a duniya na faruwar zaluncin azzalumai da yawan nuna rashin yarda ta hanyar tawaye da muzaharori da yajin aiki, da lalacewar al’amura da zai kai ga yanke kauna har sai wasu sun yi kokwanton samuwar Mahadi (A.S) da dawowar adalci duniya ta yadda yanayi zai zama ba zai juru ba, har sai ya kasance dan Adam ba shi da wani fata sai samar da da mai tseratar wa daga wajen ubangiji madaukaki wanda zai fitar da duniya daga wannan kangi da ta fada cikinsa. Wannan duk abubuwa ne da suke iya share fagen bayyanarsa (A.S) kuma zamanin neman dawowar adalci da wannan zai fara a duniya.

Amma mu sani neman adalci kawai ba ya iya sanya bayyanarsa, don haka dole ne ya zama akwai wani sharadi da zai cika wanda yake nufin samuwar wani tunani na addini ko mazhaba mai dauke da wannan fikira game da karshen zamani da kawo adalci a duniya gaba dayanta.

Wannan tunanin na neman tattaunawar kawo adalci shi ne abin da zai shagaltar da kwakwalwar mutumin karshen zamani musamman idan aka yi duba zuwa ga kishirwar adalci. Tattaunawar neman adalci da sannu zata karya tattaunawar yin zalunci a kan kasashe kuma zata raunatar da fikirar da ta doru a kai, kuma yawan masu neman adalci a cikin kowace irin al’umma zai samu karuwar karbuwa.

Wannan tunani na tattaunawa neman adalci da sannu zai mamaye tunanin mutane ya kuma share wa dan Adam hanyar yunkurin kaiwa ga samun juyin cikin rayinsa domin samar da adalci a cikin rayuwar dan Adam.

Wannan guguwar neman zata kada tare da neman yin adalci a duniya gaba daya daga gabas ta tsakiya, yayin da neman samar da adalci ya rigaya wutarsa ta huru a dukkanin sasannin duniya, dan Adam ya kasance da gaske yake wajen neman tabbatar adalci a duniya da izinin Allah.

Kuma jagoran juyin duniya zai samu karbuwa saboda masaniyarsa game da dukkan addinan Allah, kuma zai samu kaiwa zuwa ga cin nasara ta hanyar nuna musulunci a matsayin asalin addinan halittar Allah mai tsarkin ruhi.

Zai fuskanci masu zalunci domin tsayar da adalci a bayan kasa gaba daya, rundunar imam Mahadi dan Hasan Askari (A.S) zasu daga tutar neman adalci domin kaiwa ga tabbatar alkawarin Allah da ya zo a cikin kur’ani mai girma:

“Hakika mun aiko manzanninmu da dalilai kuma mun saukar da littafi da ma’auni tare da su domin mutane su tsayu da adalci, kuma mun saukar da karfe da yake da tsanani mai karfi a cikinsa da amfani ga mutane, kuma domin Allah ya san wanene zai taimake shi da manzanninsa a fake, hakika Allah mai karfi ne mabuwayi. Hadid: 25.

Juyin juya halin imam Mahadi (A.S) bai takaita da wani bangare ba, ya shafi dukkan bangarorin rayuwa da ya hada kyautata rayuwar mutane na halin tattalin arziki, da kawar da talauci, da yalwata dukiya da arziki, da kawo aminci a bayan kasa gaba daya, da warwarar matsalar al’amuran zamantakewar al’umma, da juyin neman adalci, da tabbatar da dukkan bangarorin siyasa da karfin soja, da al’adu, da wayewa, da sauaransu.

Mahadi (A.S) zai kutsa kowane bangaren rayuwar mutum kamar rana ce da bayyanarta take kawar da dukkan duhu.

Dangane da ayoyin kur’ani mai girma da ruwayoyin Shi'a musulunci shi ne ainihin shi’anci wanda yake kunshe da bayanin duniya dalla-dalla game da juyin karshen zamani:

1- Addinin adalci, (musulunci da kur’ani mai girma)

2- Jagora ma’asumi mai kawo gyara

3- Sahabbai kwamandojin jagoran duniya (su 313)

4- Masu biyayya da goyon bayan adalci (raunanan mutane)

Na Biyu- Jagoran Juyin Adalci

Bayan share fagen zuwan alamomin bayyanar wannan juyin mai girma a karshen zamani, da zai kasance ta hannun imam Mahadi dan Hasan Askari (A.S) da umarnin Allah.

Kamar yadda ya zo a kura’ani mai girma shi ne ragowar na Allah[1] kuma an zabe shi bisa sunnar Allah ta zaben bayinsa na gari. Jagoranci shi ne mai taka babbar rawa wajan kawo wannan juyin adalci na duniya.

Muhimmin abu a nan shi ne: mahangar Shi'a game da wannan al’amari a fili take, sabanin sauran mahangai da wannan mai kawo gyara jagora a wajensu ya zama mutum ne wanda ba a san shi ba. Amma a mahangar Shi'a wani mutum ne shi sananne wanda yake raye wanda Allah (S.W.T) ya tsawaita rayuwarsa kuma ya tarbiyyantar da shi kai tsaye.

Hadisai sama da 6 000 ne suka zo game da imam Mahadi (A.S) daga Shi'a da Sunna, wanda a littattafan Sunna 4 00 ne daga cikinsu suka zo, abin da yake nuna cewa; ba a taba samun wani al’amari da aka samu ruwayoyi masu yawa a dukkan al’amuran addinin musulunci game da shi ba kamar wannan al’amari[2].

Mafi yawancin ruwayoyi sun zo ne game da haihuwar wannan imami mai girma, al’amarin da yake nuna rashin yiwuwar karyar wannan ruwayoyi game da wannan hakika, ta wani bangare kuwa mun samu imaman Shi'a sun yi magana game da wannan al’amari na jagoran karshen duniya ba su taba yin shiru game da shi ba[3].

Shi'a sun yi imani da wannan jagora ma’asumi a karshen zamani wanda yake a cikin wannan duniya a raye, kuma masu sani da hakkinsa suna haduwa da shi, kuma samuwarsa ta tabbata ga mutane masu yawa ta hanyar tajriba, kuma da yawa daga mutane sun samu ganinsa da labarai masu yawa suka zo game da hakan, sun kuma rawaito labaru masu yawa game da shi (A.S).

Dadi kan haka kuma yana shiryar da wakilansa, wato malamai wadanda su ne tsaka-tsaki tsakaninsa da mutane a kan al’amura masu yawa da suka shafi fatawa da shiryarwa. Allama majlisi a littafinsa na Biharul anwar ya kawo kusan sa hannun wasikarsa a shafi 48 a babin “abin da ya zo na sa hannunsa” wanda ya hada da al’amarin fikihu da akida da sauransu[4]. Kamar yadda ya kawo shafi 118 karkashin taken “babin ambaton wanda ya gan shi (A.S)” da sauransu[5]. Bayan haka nan Allama Haji Mirza Husain Nuri ya kawo dalla-dalla na bayanin haduwa da imam Mahadi (A.S) yana mai nuni da abin da ya zo a Biharul anwar a littafin Jannatul ma’awa a shafi 117, a haduwa daban-daban har zuwa 59[6].

Hanzari ba gudu ba, muna iya cewa samuwar wannan mahanga ya sanya samuwar wasu masu da’awar karya na ganin imam Mahadi (A.S) a tsawon tarihi da muna iya ganin misalinsu kamar Sayyid Ali Muhammad bab Shirazi.

Jagoran juyi a mahangar Shi'a a karshen zamani: Ma’asumin mutum shi kadai ne jagoran dan Adam wanda yake samamme a dukkan sasannin duniya a lokaci guda wanda yake ya salladu a kan dukkan al’amuran da suke faruwa da sanin siffofinsu dalla-dalla, wanda samuwarsa ta zama dole ko a boye ko bayan bayyanarsa domin ci gaban samuwar duniya, in ba haka ba duniya zata kisfe da mutanenta ne[7].

Shi ne mai shiryar da mutanen duniya gaba daya wanda yake dauke da tutar shiriya da tsira da arzuta, da zagorancinsa ne dukkan wata tutar zata fadi kasa. A mahangar Shi'a sunansa da kinayarsa irin na Manzo ne (S.A.W), kuma shi ne cikon wasiyyai halifan Allah a bayan kasa, mai gyara kowa, ragowar na Allah, ma’abocin zamani, mai daukar fansar alayen Muhammad, mahangar Shi'a ta yi bayanin dukkan abin da ya shafe shi karara, wasu daga siffofinsa sun zo kamar haka:

1- Shi ne ya fi kowane mutum kama da Annabi ta fuskancin halitta da dabi’a.

2- Fuskarsa fara ce mai kyalli da aka cakuda da ja.

3- Yalwar goshi fari mai haske.

4- Girarsa a hade take.

5- Karan hancinsa mai siriri ne mai daukaka wanda yake da dan tudu.

6- Digo a kumatunsa na dama kamar tauraro mai walkiya.

7- Idanuwansa masu haske ne masu kaifin gani[8].

Kuma zai bayyana yana da kamanni na shekara 40 ne, al’amarin da zai yi wa wasu nauyin imani da shi.

Na Uku: Farawar Juyin Juya Hali

Ruwayoyin Shi'a da Sunna[9] sun zo game juyin imam Mahadi (A.S) wanda zai zo bayan cikar mukaddimominsa da shiryawar duniya don karbarsa, wanda zai fara daga Makka. Kuma za a yi bishara da shi ta hanyar sauti mai tsawa daga sama da safe kamar yadda ya zo a wasu ruwayoyi, da kuma tsawa ta biyu daga yamma bayan faduwar rana ko kuma ranar da take biyo wa bayan taron ma’abota bata da barna[10].

Game da farawar wannan juyin Imami na biyar yana cewa: “Na rantse da Allah! ina ganin sa ya bayyana yana mai jingina da Hajarul aswad yana ce: Ya ku mutane mu muna neman taimakon kowa a kan mutanen da suka zalunce mu, kuma suka kwace mana hakkinmu… Ni ne marayan Adam, a jiyar Nuh, zabin Ibrahim…[11]

A farkon bayyanar imam (A.S) zai yi hudubarsa[12] mai tarihi tsakanin rukunin hajarul aswad da makamu Ibrahim (A.S), kuma farkon wanda zai yi masa bai’a shi ne Jibril (A.S) bayan nan sai sahabbansa 313, kamar yadda ya zo daga imam Bakir (A.S)[13].

Sai dai wasu littattfai sun ambaci inda zai bayyana da cewa a wani kauye ne mai suna “Kur’a” a Yaman, wannan al’amari ya zo a littattafai kamar Albayan, da Alhawi, da Kashful gumma, da Al’malahim wal fitan[14]. Kamar yadda aka samu wasu ruwayoyi sun yi nuni da cewa daga birnin Kum ne motsinsa na juyi zai fara[15].

Sannan domin yada juyinsa sai ya fita daga Makka yayin da mutane dubu goma zasu yi masa kawanya kamar ta zobe, Jibrilu yana damansa, Mika’ilu yana hangunsa, sannan sai ya kada tutar Manzon Allah yana sanye da sulkensa, a hannunsa akwai takobin zulfikar[16].

Daga nan ne zai doshi Madina sannan sai Kufa wacce ita ce hedkwatar imam Mahadi (A.S), abin da ake nufi da Kufa ya hada har yankin Najaf.

Da farko Sufyani wanda yake daga alayen Abu sufyan zai zo Kufa wajan imam (A.S) da sunan sulhu, kuma mutanen Najaf da Kufa zasu karbi jagorancin imam Mahadi (A.S) su nemi tsayar da sallar jumma’a a bayansa, al’amarin da zai tunatar da su sallar Annabi (S.A.W), daga nan ne motsin juyi da neman ‘yanci zai fara, juyi ya rika daduwa a kowace rana[17].



[1] Hudu: 86. Naml: 59. Fadir: 32. Maryam: 58. Hajj: 75. Ali imran: 33, 42.

[2] Shahid Sayyid Muhammad Bakir Sadar, Inkilabu Mahadi Wa Fandar Tarjamar Sayyid Ahmad Alamul Huda, Shafi 152 – 163.

[3] Biharul Anwar, Jildi 13, J 15, Shafi 65 – 162.

[4] Da jildi 13, j: 53.

[5] Littafin da ya gabata, shafi: 1 – 89, 151- 180.

[6] Littafin da ya gabata, shafi: 200 – 317.

[7] Sayyid Muhammad Sadar, Tarihi Ma Ba’adazzuhur, Shafi: 48 – 57.

[8] Kamar Muhyiddin Bn Arabi, Alfutuhatul Makiyya, J 3, Shafi: 327.

[9] Abu Dawud J 2, Shafi 423, da Suyudi, Alhawi, J 2, Shafi: 102, 129, 150, 152, 174, 341.

[10] Kamil Sulaiman, Ruzegare Rahayi, J 2, Shafi: 865 – 874.

[11] Littafin Da Ya Gabata, J 1, Shafi: 482 – 484.

[12] Muhamamd Sadar, Tarihi Ma Ba’adaz Zuhur, Shafi: 335 – 339.

[13] Littafin da ya gabata, Shafi: 484.

[14] Muhammad Sadar, Tarihi Ma Ba’adaz Zuhur, Shafi: 335 – 339.

[15] Anwarul Mush’ash’in, J 1, Shafi: 453.

[16] Ruzegare Rahayi, j 1, shafi: 485.

[17] Tarihi ma ba’adaz zuhur, shafi: 443 – 450. Da sauran littattafai kamar: Yanabi’ul Mawadda.