Kira Zuwa Ga Hadin Kai A Musulunci



Kira Zuwa Ga Hadin Kai A Musulunci

An san Ahlul Baiti (AS) da kwadayinsu a kan wanzuwar addinin musulunci, da kira zuwa ga daukakarsa da hada kan mabiyansa, da kiyaye ‘yan’uwantaka a tsakaninsu, da cire mugun kuduri daga zukatansu, da kullace-kullace daga rayukansu, ba za a mance da matakin Amirul Muminin Aliyyu dan Abi Talib (AS) game da halifofin da suka gabace shi ba, duk da fushin da ya yi da su da kuma yakininsa da kwacewarsu ga hakkinsa, amma sai ya tafi tare da su, ya zauna lafiya da su, kai an boye ra’ayinsa na cewa shi ne wanda aka yi wasiyya da halifancinsa, har ya zama bai bayyana nassin ba a bainar jama’a har sai da al’amarin ya koma hannunsa, sannan ya kafa hujja da sauran wadanda suka rage daga cikin Sahabbai game da al’amarin nassin Al-Ghadir a ranar Rahba da ta shahara. Ya kasance ba ya boye shawara garesu game da abin da ya shafi musulmi ko Musulunci na amfani da maslaha, saudayawa yana fada game da wannan al’amari: “Sai na ji tsoron idan ban taimaki Musulunci da ma’abotansa ba zan ga gibi a cikinsa ko rushewa”.

Kamar yadda babu wani abu da ya taba zowa daga gareshi wanda zai yi tasiri a karfafa mulkinsu, ko raunana jagorancnsu, ko rage kwarjininsu, sai ya kuntata wa kansa, ya zauna a gida duk da abin da yake gani daga gare su. Dukkan wannan saboda kiyaye maslahar Musulunci ta gaba daya, da kiyaye kada a ga wani gibi a Musulunci ko rushewa, har aka san haka daga gare shi, kuma halifa Umar dan Haddabi ya kasance yana fada yana kuma maimaitawa: “Kada na kasance cikin wani al’amari mai wuyar sha’ani da Abul Hasan ba ya ciki.” Ko fadinsa: “Ba don Ali (A.S) ba da Umar ya halaka”.

Haka nan ba za a mance da matakin Imam Hasan dan Ali (AS) ba dangane da yin Sulhu da Mu’awiya, bayan ya ga cewa dagewa a kan yaki zai shafe ya kuma kawar da Alkawari mafi girma –Kur’ani- da adalci har ma da musulunci daga samuwa har zuwa karshen zamani, a kuma shafe shari’ar Ubangiji, a kuma gama da wadanda suka yi saura daga Zuriyar Manzo daga Ahlul Baiti, sai ya fifita kiyaye zahirin Musulunci da sunan Addini, duk da ya yi sulhu da Mu’awiya babban makiyin Addini da ma’abotansa, mai husuma mai mugun kuduri ga imam Hasan (A.S) da shi’arsa, tare da abin da ake tsammani na faruwar zalunci da kaskanci gareshi shi da mabiyansa, ga kuma takubban Banu Hashim da na shi’arsa a zazzare ba sa son komawa ba tare da sun yi aikinsu na kariya da gwabzawa ba, sai dai maslahar musulunci madaukakiya ita ce ta fi dukkan wadannan al’amuran.

Amma Shahidi Imam Husain (AS) idan ya motsa to domin ya ga cewa idan aka ci gaba da halin da ake ciki, Banu Umayya ba su sami wanda zai tona asirinsu ba, to da sannu zasu shafe sunan Musulunci, su kawar da darajarsa, sai ya so ya tabbatar wa tarihi ketare iyakarsu, ya fallasa abin da suke kulla wa Shari’ar Manzon Allah (S.A.W). Ba don yunkurinsa mai albarka ba, da Musulunci ya zama wani labari ne da tarihi zai rika ambatonsa tamkar wani addinin barna. Kwadayin Shi’a a kan raya ambatonsa ta hanyoyi daban- daban ya zamanto saboda kammala sakon da yunkurinsa na dauki-ba-dadi da zalunci ne, kuma domin raya al’amarinsa na cika umarni da biyayya ga Imamai (A.S)[1].

A nan kwadayin Ahlul Baiti (A.S) na wanzuwar izzar musulunci zata bayyana garemu koda kuwa mai mulki ya kasance mafi tsananin makiyansu ne a matakin Imam Zainul Abidin (A.S) da sarakunan Banu umayya alhalin sun maraita shi, an keta alfarmarsa a lokacinsu, kuma yana mai yawan bakin cikin a kan abin da suka yi wa babansa da Ahlin gidansa a waki’ar karbala, amma duk da haka yana yi wa rundunar musulmi addu’a da nasara, musulunci kuma da izza, musulmi kuma da yalwa da aminci, kuma ya riga ya gabata cewa makaminsa kawai wajen yada ilimi Shi ne addu’a, ya koya wa Shi’a yadda zasu yi addu’a ga sojojin Musulunci da musulmi, kamar addu’arsa da aka sani da “Addu’ar masu dakon iyaka” wacce yake cewa a cikinta: Ya Allah! ka yi tsira ga Muhammad da Zuriyar Muhammad, ka yawaitasu, ka kaifafa makamansu, ka kare matattararsu, ka kange iyakarsu, ka hada taronsu, ka shirya al’amarinsu, ka kadaita da wadatar da bukatunsu, ka karfafa su da cin nasara, ka taimake su da hakuri”. Zuwa inda yake cewa: “Ya Allah ka karfafa guraren Musulunci da haka, ka kiyaye gidajensu da shi, ka yawaita dukiyarsu da shi, ka shagaltar da su gabarin yakarsu don su dukufa ga ibadarka, da hana kai musu farmaki don su kadaita da kai, har ya zamanto ba a bauta wa kowa a bayan kasa sai kai, kuma ba a sanya wa goshi kasa saboda wani sai kai.” Haka nan ya ci gaba da addu’arsa mai fasaha, -kuma tana daga mafi tsawon addu’o’insa- wajen fuskantar da sojojin musulmi zuwa ga abin da ya kamace su na daga kyawawan dabi’u, da kuma shirya kansu, da tanadi a kan makiya, ta kunshi dukkan darussan yaki na jihadin Musulunci da bayanin manufarsa da fa’idarsa, kamar kuma yadda take fadakar da musulmi da irin gargadi da takatsantsan dangane da makiyansu, da abin da ya wajaba su yi riko da shi a mu’amalarsu da kariyar kansu, da kuma abin da ya wajaba a kansu game da yankewa daga komai zuwa ga Allah baki daya, da nisantar abubuwan da ya haramta, da yin abu saboda girman zatinsa.

Haka nan sauran imamai (A.S) a matakansu da suka dauka game da sarakunan lokutansu, duk da sun sami takurawa daga garesu iri-iri, da kuma azabtar da su da dukkan nau’i na kekasar zuciya da tsanantawa, domin su yayin da suka san cewa hukumar adalci ba za ta dawo hannunsu ba, sai suka juya zuwa ga koya wa mutane al’amuran Addininsu, suna fuskantar da mabiyansu fuskantarwa ta addini madaukaki. Dukkan wani yunkuri da ya faru a zamaninsu daga bangaren Alawiyyawa da wasunsu, bai kasance da ishararsu da son su ba, ya ma saba wa umarninsu da karfafawarsu ne a fili, duk da cewa sun fi kowa kwadayin kafa hukumar musulunci hatta sun fi Abbasawa son haka su kansu.

Ya isa garemu mu karanta wasiyyar Imam Musa Alkazim (AS) ga shi’arsa: “Kada ku kaskantar da kawukanku da barin biyyyar shugabanku, idan ya kasance mai adalci to ku roki Allah wanzuwarsa, idan kuwa ya kasance azzalumi to ku roki Allah gyaransa, domin gyaruwarku na cikin gyaruwar shugabanku, kuma shugaba adali yana matsayin uba mai rahama ne, ku so masa abin da kuke so wa kanku, kuma ku ki masa abin da kuke ki wa kanku”[2].

Wannan ita ce matukar abin da ake siffantawa na kiyayewar al’umma ga amincin shugaba da su so masa abin da suke so wa kansu, su ki masa abin da suke ki wa kansu.

Bayan duk wannan muna cewa: Alhakin shi’a da wasu marubuta na wannan zamani suke dauka ya girmama! Yayin da suke siffanta shi’a da cewa ita kungiya ce ta asiri mai barna, ko kuma wata jama’a ce ta ‘yan juyin juya hali. Haka nan cewa wajibi ne a kan mabiyin koyarwar Ahlul Baiti (A.S) ya ki zalunci, da azzalumai, da fasikai, ya yi duba zuwa ga mataimakansu duba na kyama, da rashin yarda, da wulakanci, wannan dabi’a ba ta gushe ba suna gadonta jikoki da ‘ya’ya, amma sam ba ya daga dabi’arsu su yi yaudara ko cin amana, kuma ba tafarkinsu ba ne yin juyin juya hali, ko su yi tawaye a kan jagorancin da yake an kafa shi da sunan musulunci, ko a boye ko a sarari.

kuma ba sa halattawa kansu kisan gilla ko afka wa musulmi ko wace irin Mazhaba ko Darika yake bi, wannan kuwa domin rikonsu ne da koyarwar Ahlul Baiti (A.S), kuma duk musulmin da ya yi kalmar shahada biyu a wajansu, dukiyarsa da jininsa kubutattu ne, kuma cin mutuncinsa haramun ne; “Dukiyar mutum musulmi ba ta halatta sai da son ransa”. Musulmi dan’uwan musulmi ne, kuma yana da hakkoki a kansa kamar yadda bahasi mai zuwa zai yi bayani”.



1 next